Akalla mutane 60 ne da suka hada da kananan yara suka mutu a India a ranar Lahadi, yayin da wata gada ta rufta a yammacin jihar Gujarat, lamarin da ya sa daruruwan mutane suka tsunduma cikin ruwa.
A cewar karamin minista a ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi na Gujrat, Brijjesh Merjabut, an gyara gadar kwanan nan, don haka, dole gwamnati za ta binciki dalilin musabbabin afkuwar lamarin.
Ya kara da cewa, a halin yanzu gwamnati ta mayar da hankalinta ne kan ayyukan ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
Da yake magana da NDTV a wata hira daga wurin da lamarin ya faru, ya ce akalla mutane 17 ne ake jinyarsu yanzu haka a asibiti. Akwai kananan yara da dama a cikin wadanda suka mutu.
Iyalan wadanda abin ya shafa za su sami tallafin kudi daga asusun ba da agaji na Fira minista, a cewar Fira Ministan India Narendra Modi.