Salon yaƙin neman zaɓe yana zuwa da wasu sauye-sauye, inda abubuwan da a da ba a cika damuwa da su ba, yanzu mutane suna mayar da hankali akansu.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Allah-Wadai Da Hare-Hare Da Kwacen Wayoyi Da Magoya Bayan NNPP Ke Yi
- Kwankwaso Zai Bayyana Manufofin Takararsa A Ranar 1 Ga Watan Nuwamba
Lokaci ya rage ƙasa da ‘yan watanni a gudanar da babban zaɓe a Najeriya, hukumomi da ƙungiyoyin cikin gida da na ƙetare na shirya tarukan mahawara a tsakanin ‘yan takarar gwamnonin jihohi da kuma masu neman shugabancin ƙasar nan domin ba su damar bayyana wa masu zaɓe irin abubuwan da suka ƙuduri aniyar aiwatarwa idan aka zaɓe su.
A jihar Kano dake Arewacin Nijeriya, a makon da ya gabata mashahuriyar Ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya, wato The Nigerian Medical Association, NMA, reshen jihar ta shirya wa masu neman takarar gwamna a zaɓen shekarar 2023 muhawara ta musamman akan irin tanadin da su ka yi wa ɓangaren kiwon lafiya ga miliyoyin jama’ar jihar.
Muhawarar da NMA ta shirya ta kasance cikin jerin abubuwan da take yi na bikin makon likitoci na 2023. A kuma irin jawaban da shugaban ƙungiyar ya yi, an ji shi yana ambato cewa likitoci 533 ne kaɗai suke aiki a ƙarƙashin gwamnatin jihar Kano, wanda hakan abin takaici ne ƙwarai da gaske.
Me Yasa Abba Kabiru Yusuf Ya Ƙaurace Wa Muhawarar?
‘Yan takarar da suka hallarci muhawarar sun haɗa da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC, da Salihu Tanko Yakasai na jam’iyyar PRP da Bashir I. Bashir na jam’iyyar Labour Party da kuma Malam Ibrahim Khalil na jam’iyyar ADP.
Sai dai ɗan takarar jam’iyyar NNPP a jihar, Abba Kabiru Yusuf bai hallarci zauren muhawarar ba. A lokacin muhawarar, ‘yan takarar sun faɗi abubuwa da dama da za su kawo ci gaba a jihar Kano a ɓangaren kiwon lafiya.
Ƙin halartar Abba Kabiru Yusuf yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba za a yi mantawa da shi ba a wannan muhawarar, musamman ganin yadda aka riƙa dakon zuwansa daga farkon fara muhawarar har aka kai ƙarshe, amma bai halarta ba.
Sai dai a wata sanarwa da kakakinsa, Ahmad Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce ɗan takarar bai samu halartar muhawarar ba ne saboda samun gayyatar ta NMA a ƙurarren lokaci.
Haƙiƙa idan har ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Gawuna zai samu damar halartar wannan muhawara da NMA ta shirya to haƙiƙa Abba Kabiru Yusuf ne ya fi cancanta a ce ya je zauren muhawarar akan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda a ɗan lokacin nan kafafen yaɗa labarai ( musamman gidajen Rediyo masu zaman kansu) su ka yi ta rahotanni akan yadda ɓangaren kiwon lafiya a jihar ke ci gaba da fuskantar ƙalubale da koma baya da kuma rashin ma’aikata— abin da ke haifar da asarar rayukan al’ummar jihar.
Haka kuma rashin halartar muhawarar da Abba Kabiru Yusuf ɗin ya yi ya jefa al’ummar jihar Kano cikin shakku da tantamar dacewar ɗan takarar gwamnan a jam’iyyar NNPP. Domin a zahirin gaskiya, yadda magoya bayan jami’yyar ke bayyana irin ayyukan da tsohon gwamnan Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wa jihar Kano, bai kamata a ce Abba ɗin ya noƙe ba domin yana da abin faɗa.
Wata majiya ta tabbatar da cewa Abba Kabiru Yusuf ɗin na daga cikin waɗanda su ka samu katin gayyatar akan lokaci, wanda hakan yana da nasaba da wasu likitoci ‘yan Kwankwasiyya da suke da kusanci da shi kuma su ka bayar da tabbaci akan zai halarci zauren muhawarar amma sai ya watsa musu ƙasa a ido.
Hakazalika, ba wannan ne karon farko da Abba Kabiru Yusuf ɗin ya kaurace wa irin wannan muhawarar ba domin a halin da ake ciki, akwai wata mashahuriyar ƙungiya da ta kasance mai zaman kanta kuma take samun tallafi daga ƙasar Birtaniya da take son ganawa da Abba Gida Gida amma abin ya faskara.
Ƙungiyar da ta ke ƙunshe da manyan mutane masu ilimi kuma ‘yan asalin jihar Kano, ta buƙaci ganin Abba Kabiru Yusuf ɗin ne kamar yadda su ka ga sauran ‘yan takarar gwamnan Kano a jam’iyyu daban-daban domin gabatar masa da kundin buƙatar al’ummar jihar Kano da suke muradi ga duk wanda ya samu nasarar zama gwamna a shekarar 2023, sai dai lamarin ya gagari Kundila.
Wannan ƙungiya fiye da sau biyar tana rubutawa Abba Gida Gida takardar neman izini akan ya ba su dama domin su gabatar masa da buƙatar al’ummar jihar Kano mai mutum miliyan 9,401,288, amma har yanzu babu amsa daga ɓangarensa.
Babu shakka irin wannan halin ko – in -kula da Abba Kabiru Yusuf da jami’yyar sa ta NNPP suke nuna wa al’umma yana alamta wa miliyoyin masu zaɓe cewa ba su shirya magance matsalolin da Kanon ke fuskanta ba, musamman ta fuskar ilimi da farfaɗo da masana’antu da kiwon lafiya da samar da ruwan sha a yankunan birane da karkara, da gina hanyoyi da bunƙasa harkokin noma da kuma inganta kasuwanci ya tafi daidai da zamanin da duniya ke yayi.
Buhari Abba ya rubuto daga Kano – Nijeriya
[email protected]