Mutum biyu sun rasa rayukansu a wani harin nakiya da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna.
Harin ya faru ne a jiya Alhamis da misalin karfe 2 na rana bayan da mutanen biyu suke tuka mota, inda suka taka nakiyar da ake zargin ‘yan bindigar ne suka dasa a wani yanki da ake kira Zangon Tofa a Kabrasha da ke a karamar hukumar Chikun.
- Sauya Kudi Kokari Ne Na Haramta Amfani Da Naira – Sunusi Ata
- 2023: Kotu Ta Tabbatar Da Uba Sani A Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC A Kaduna
Kwamishinan tsaron harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne, ya sanar da cewa, mutanen biyu, sun rasu ne bayan sun yi safarar kayan amfanin gonarsu, inda ya sanar da sunayen mamatan Babajo Alhaji Tanimu da kuma Safiyanu Ibrahim.
Gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan biyu tare da yin kira ga al’ummar da ke yankin da su kwatar da hankalinsu.
Jihar Kaduna dai, na daya daga cikin jihohin a yankin Arewa maso Yamma da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga tare da kuma yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, inda hakan ya janyo wasu al’umomi da dama da hare-haren ya yi kamari, suka tsere daga matsugunansu.
Duk da yawan tabbacin da gwamnatin jihar da kuma tabbacin hukumomin tsaro da ke jihar kan magance kalubalen rashin tsaro, ‘yan bindigar na ci gaba da kai hare-haren su, inda hakan ke kara jefa tsoro a zukatan jama’a, musamman ganin zaben 2023 na karatowa.