Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal ta kori ‘yan takarar majalisar wakilan tarayya na jam’iyyar Labour Party a mazabar Fatakwal ta 1 da ta 2 gami da mazabar dan majalisar tarayya ta Obio/Akpor.
Jam’iyyar PDP ce ta garzaya kotun domin kalubalantar zaben fidda-gwanin jam’iyyar LP ta gudanar a mazabukan ‘yan majalisar tarayyar uku.
- An Yi Bikin Budewar CIIE Karo Na 5 A Birnin Shanghai
- Wata Mata Ta Kashe Dan Hayar Da Ke Gidanta A Ondo
A hukuncin da alkalin kotun, mai shari’a Stephen Daylop-Pam ya yanke, ya ce ‘yan takarar uku ba su samu nasara ta hanyar gudanar da sahihin zabe da doka ya tanadar ba.
Sai dai kuma jagororin jam’iyyar LP a jihar sun misalta hukuncin a matsayin mai cike da kura-kurai kuma akwai son zuciya a cikinsa.
Shugaban jam’iyyar LP a jihar, Dienye Pepple, a sanarwar manema labarai da ya fitar a jiya a Fatakwal ya ce, wadanda abun ya shafa tuni aka sauya su.
Sanarwar ta ce: “Abu ne kawai a zahirance kuma a fayyace cewa PDP na son yin takarar nan ita kadai sannu a hankali tana kai dukkanin sauran jam’iyyu zuwa kotu da nufin da hana kowa takara sai ita.
“A mu jam’iyyar ta LP gaba daya wannan hukuncin bai yi wakilin ba, su wadanda lamarin ya shafa tunin aka canza su, amma jam’iyyar mu tana shirye-shiryen daukaka kara kuma muna da yakin adalci zai wanzu kuma zai bayyana.”
Ya nuna kwarin guiwarsa na cewa jam’iyyarsa za ya ci zabe a 2023 koda PDP ba ta so ba.