Daliban shirin ‘N-Build’ kashi na ‘C1’ sun samu horo, tare da kayan aiki.
Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa horaswar da aka ba daliban shirin ‘N-Build’ kashi na ‘C1’ za ta amfane su a tsawon rayuwar su, kuma a duk inda su ka shiga.
Ministar ta bayyana haka ne a wajen bikin yaye daliban da su ka ci gajiyar shirin, kashi na ‘C1’, wanda aka yi a ranar Laraba a Abuja.
An yi watanni uku ana horas da waɗanda su ka shiga tsarin, wanda aka yi a karkashin shirin nan na Gwamnatin Tarayya na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, wato ‘National Social Investment Programme’ (NSIP) da kuma shirin ‘N-Power’.
A wajen bikin, ministar ta kuma raba kayan aiki ga dukkan wadanda aka yaye a wata makarantar koyar da sana’o’i mai suna ‘FOCI Skills Academy’ da ke unguwar Katampe a Abuja.
A taron, Hajiya Sadiya ta yi la’akari da cewa wannan horaswa ko tirenin da aka yi, an yi irin sa a wasu cibiyoyi har 693 a faɗin kasar nan da nufin karfafa wa matasan da ba su da aikin yi gwiwa domin su samu kwarewar yin sana’a da za ta taimaki rayuwar su.
Ta ce masu, “Kwarewar da ku ka samu wajen horaswar a watanni uku da su ka gabata za ta kasance muhimmiyar hanyar da za ta taimake ku a yau da kuma gobe a kowane tsarin tattalin arziki na duniya.
“Wannan ma’aikata, tare da shugabannin gudanar da shirin NSIP da ‘N-Power’ da sauran cibiyoyin da abin ya shafa, sun yi aiki tukuru don tabbatar da cewa wannan abu ya taimaka wajen rage bukatar da ake yi ta kwararrun da aka horas don daukar su aiki.
“A wannan aji na ‘C1’ na shirin ‘N-Build’, an yaye dalibai ne domin su fara zama karkashin wasu masu irin sana’ar su, kamar yadda mai girma Shugaban Kasa ya Kudurci samar da karin ayyukan yi da hanyoyin samun arziki ga dimbin matasa. Za a tura su zuwa wurare daban-daban inda za su fara ayyukan su.
“Sannan su ma ‘yan aji na C2 na shirin ‘N-Power’, nan da makonni kaɗan za a tura su cibiyoyin horaswa, wanda duk manufar dai ita ce a tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara.”
Ministar ta bayyana cewa an sama wa kowanne daga cikin masu cin moriyar shirin kunshin kayan aiki da kayan tsaron lafiyar jiki a wajen aiki, da kayan zuwa wajen horaswa don a ba su damar yin aiki a matsayin kwararrun masu sana’a da aka horas.
Ta yi kira a gare su da su yi amfani sosai da horaswar da aka ba su.
Hajiya Sadiya ta ce: “Tunda har kun gama horaswar cikin gida, za a hada ku kai-tsaye da hukumomin da su ka dace domin zaman koyo da za ku yi da su na tsawon wata shida.
“Wannan zaman koyon zai ba ku damar samun ilimin aiki, wanda za a fara shi daga ranar Litinin, 13 ga Yuni, 2022.
“A lokacin wannan zaman koyon na watanni shida, za a duba aikin ku tare da auna shi, wanda Cibiyar Magina ta Nijeriya Mai Rajista (Council of Registered Builders of Nigeria, CORBON) da Cibiyar Tsara Kayan Ƙirƙira ta Ƙasa (National Automotive Design and Development Council, NADDC) da kuma Hukumar Ƙwararru ta Masu Aikin Yawon Shaƙatawa ta Nijeriya (Institute of Tourism Professionals of Nigeria, ITPN) su za su yi maku.”
Ɗaliban da aka yaye ɗin dai sun samu horo ne a fagagen gyaran mota, fasahar aikin gona, aikin kafinta, aikin haɗa wutar lantarki, aikin gini da sa tayil, aikin famfo da shimfiɗa fayif.
Haka kuma ministar ta je Gidauniyar Cibiyar Masana’antu (Industrial Trust Fund Centre) domin miƙa ƙunshin kayan aiki da kayan fara sana’a ga ɗaliban da aka yaye a fagen sana’ar yawon buɗe ido, waɗanda su ka haɗa da koyon tuya da haɗa alawa, dafa abinci, kula da gida da kimtsa shi, da kuma dabarun haɗa abin sha.
Waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabiru Bala, da Darakta-Janar na Hukumar Magina ta Ƙasa (Federation of Construction Industry), Mista Olubunmi Adekoje, da Babban Kodineta na Shirin NSIP, Dakta Umar Bindir, da shugaban masu aiwatar da shirin ‘N-Power’, Mista Nsikak Okon, da sauran manyan baƙi.