• Leadership Hausa
Monday, October 2, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daliban Shirin ‘N-Build’ Kashi Na ‘C1’ Sun Samu Horo Tare da Kayan Aiki

by Sulaiman
1 year ago
in Labarai
0
Daliban Shirin ‘N-Build’ Kashi Na ‘C1’ Sun Samu Horo Tare da Kayan Aiki
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Daliban shirin ‘N-Build’ kashi na ‘C1’ sun samu horo, tare da kayan aiki.

Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa horaswar da aka ba daliban shirin ‘N-Build’ kashi na ‘C1’ za ta amfane su a tsawon rayuwar su, kuma a duk inda su ka shiga.

Ministar ta bayyana haka ne a wajen bikin yaye daliban da su ka ci gajiyar shirin, kashi na ‘C1’, wanda aka yi a ranar Laraba a Abuja.

An yi watanni uku ana horas da waɗanda su ka shiga tsarin, wanda aka yi a karkashin shirin nan na Gwamnatin Tarayya na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, wato ‘National Social Investment Programme’ (NSIP) da kuma shirin ‘N-Power’.

A wajen bikin, ministar ta kuma raba kayan aiki ga dukkan wadanda aka yaye a wata makarantar koyar da sana’o’i mai suna ‘FOCI Skills Academy’ da ke unguwar Katampe a Abuja.

Labarai Masu Nasaba

Ilimin ‘Ya’ya Mata: Kano Ta Fara Bai Wa ‘Yan Mata 45,000 Tallafin N20, 000

Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

A taron, Hajiya Sadiya ta yi la’akari da cewa wannan horaswa ko tirenin da aka yi, an yi irin sa a wasu cibiyoyi har 693 a faɗin kasar nan da nufin karfafa wa matasan da ba su da aikin yi gwiwa domin su samu kwarewar yin sana’a da za ta taimaki rayuwar su.

Ta ce masu, “Kwarewar da ku ka samu wajen horaswar a watanni uku da su ka gabata za ta kasance muhimmiyar hanyar da za ta taimake ku a yau da kuma gobe a kowane tsarin tattalin arziki na duniya.

“Wannan ma’aikata, tare da shugabannin gudanar da shirin NSIP da ‘N-Power’ da sauran cibiyoyin da abin ya shafa, sun yi aiki tukuru don tabbatar da cewa wannan abu ya taimaka wajen rage bukatar da ake yi ta kwararrun da aka horas don daukar su aiki.

“A wannan aji na ‘C1’ na shirin ‘N-Build’, an yaye dalibai ne domin su fara zama karkashin wasu masu irin sana’ar su, kamar yadda mai girma Shugaban Kasa ya Kudurci samar da karin ayyukan yi da hanyoyin samun arziki ga dimbin matasa. Za a tura su zuwa wurare daban-daban inda za su fara ayyukan su.

“Sannan su ma ‘yan aji na C2 na shirin ‘N-Power’, nan da makonni kaɗan za a tura su cibiyoyin horaswa, wanda duk manufar dai ita ce a tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara.”

Ministar ta bayyana cewa an sama wa kowanne daga cikin masu cin moriyar shirin kunshin kayan aiki da kayan tsaron lafiyar jiki a wajen aiki, da kayan zuwa wajen horaswa don a ba su damar yin aiki a matsayin kwararrun masu sana’a da aka horas.

Ta yi kira a gare su da su yi amfani sosai da horaswar da aka ba su.

Hajiya Sadiya ta ce: “Tunda har kun gama horaswar cikin gida, za a hada ku kai-tsaye da hukumomin da su ka dace domin zaman koyo da za ku yi da su na tsawon wata shida.

“Wannan zaman koyon zai ba ku damar samun ilimin aiki, wanda za a fara shi daga ranar Litinin, 13 ga Yuni, 2022.

“A lokacin wannan zaman koyon na watanni shida, za a duba aikin ku tare da auna shi, wanda Cibiyar Magina ta Nijeriya Mai Rajista (Council of Registered Builders of Nigeria, CORBON) da Cibiyar Tsara Kayan Ƙirƙira ta Ƙasa (National Automotive Design and Development Council, NADDC) da kuma Hukumar Ƙwararru ta Masu Aikin Yawon Shaƙatawa ta Nijeriya (Institute of Tourism Professionals of Nigeria, ITPN) su za su yi maku.”

Ɗaliban da aka yaye ɗin dai sun samu horo ne a fagagen gyaran mota, fasahar aikin gona, aikin kafinta, aikin haɗa wutar lantarki, aikin gini da sa tayil, aikin famfo da shimfiɗa fayif.

Haka kuma ministar ta je Gidauniyar Cibiyar Masana’antu (Industrial Trust Fund Centre) domin miƙa ƙunshin kayan aiki da kayan fara sana’a ga ɗaliban da aka yaye a fagen sana’ar yawon buɗe ido, waɗanda su ka haɗa da koyon tuya da haɗa alawa, dafa abinci, kula da gida da kimtsa shi, da kuma dabarun haɗa abin sha.

Waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabiru Bala, da Darakta-Janar na Hukumar Magina ta Ƙasa (Federation of Construction Industry), Mista Olubunmi Adekoje, da Babban Kodineta na Shirin NSIP, Dakta Umar Bindir, da shugaban masu aiwatar da shirin ‘N-Power’, Mista Nsikak Okon, da sauran manyan baƙi.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Matashin Dan Wasa Gavi Ya Kafa Tarihi A Tawagar Sifaniya

Next Post

Manoma Sun Koka Kan Hauhawar Farashin Takin Zamani

Related

Mata
Manyan Labarai

Ilimin ‘Ya’ya Mata: Kano Ta Fara Bai Wa ‘Yan Mata 45,000 Tallafin N20, 000

2 hours ago
Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu
Labarai

Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

10 hours ago
Tinubu
Labarai

Ranar ‘Yanci: Tinubu Ya Kara Wa Kananan Ma’aikata N25,000 Kan Albashinsu

12 hours ago
BUA
Manyan Labarai

Daga Gobe 2 Ga Oktoba Farashin Buhun Simintin BUA Ya Koma N3,500 – Kamfanin

14 hours ago
Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya
Labarai

Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya

15 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Yaba Da Ayyukan Bello Koko Na Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kafa Sashi Na Musamman A NPA Don Inganta Ayyukanta

18 hours ago
Next Post
Manoma Sun Koka Kan Hauhawar Farashin Takin Zamani

Manoma Sun Koka Kan Hauhawar Farashin Takin Zamani

LABARAI MASU NASABA

Mata

Ilimin ‘Ya’ya Mata: Kano Ta Fara Bai Wa ‘Yan Mata 45,000 Tallafin N20, 000

October 2, 2023
Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

October 1, 2023
Tinubu

Ranar ‘Yanci: Tinubu Ya Kara Wa Kananan Ma’aikata N25,000 Kan Albashinsu

October 1, 2023
Hangzhou

Birnin Hangzhou Ya Samu Karuwar Masu Yawon Bude Ido Albarkacin Gasar Wasanni Ta Asiya Dake Gudana

October 1, 2023
Syria

Shugaban Syria: Manyan Tsare-tsare Uku Na duniya Su Ne Jagororin Sabuwar Duniya

October 1, 2023
BUA

Daga Gobe 2 Ga Oktoba Farashin Buhun Simintin BUA Ya Koma N3,500 – Kamfanin

October 1, 2023
Kasar Sin

Ofishin Jakadancin Kasar Sin Dake Najeriya Ya Shirya Bikin Murnar Cikar Sin Shekaru 74 Da Kafuwa

October 1, 2023
Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya

Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya

October 1, 2023
Amurka

Amurka Ita Ce “Daular Karya”Ta Ko Wace Fuska

October 1, 2023
Gwamnatin Tarayya Ta Yaba Da Ayyukan Bello Koko Na Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kafa Sashi Na Musamman A NPA Don Inganta Ayyukanta

October 1, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.