Wasu ‘yan mahara sun kai wa dakarun sojoji da ke sintiri a unguwar Izombe, a karamar hukumar Oguta a Jihar Imo.
Kakakin rundunar, Kaftin Joseph Akubo ne, ya tabbatar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Owerri a ranar Litinin.
- Za A Sake Gwabzawa Da Madrid Da Liverpool A Zagayen 16 Na Kofin Zakarun Turai
- Kamfanin PowerChina Ya Samarwa Kauyen Lauteye Dake Najeriya Na’urar Samar Da Wutar Lantarki Bisa Hasken Rana
Akubo ya ce lamarin ya faru ne bayan an tura sojoji zuwa ga al’umma masu arzikin man fetur domin su tabbatar da komowar matasan yankin da kuma sauran laifukan da ke faruwa a yankin.
Ya ce, “Sojojin suna sintiri ne a yankin, sai suka fuskanci harin da wasu matasa dauke da makamai.
“Kwanaki biyu da suka wuce, an kashe wani direban babbar mota, tare da wasu miyagun ayyukan da ya sa aka kara sintiri.
“Sojojin na cikin sintiri na yau da kullum lokacin da aka kai musu harin.”
Sai dai Akubo ya ce har yanzu bai tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba saboda har yanzu matasan na ci gaba da fafatawa da sojojin.
Ya kara da cewa, “Ba zan iya fada muku adadin wadanda suka mutu ba saboda har yanzu matasa dauke da makamai suna kai hari ga mutanenmu da ke fakewa a gine-gine a unguwar.”