A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci cibiyar ba da umurni ta hadin gwiwa, ta hukumar kolin rundunar sojojin kasar ko CMC, don bayyana matsayin sabuwar hukumar kolin rundunar sojojin kasar game da aiwatar da tsare tsaren da aka amince da su, yayin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) karo na 20 da ya gudana a kwanan baya, da karfafa horas da dakarun sojin kasar, da inganta shirin su na tunkarar duk wani matakin soji. (Saminu Alhassan)