Ana nuna wasu sabbin kayayyakin da a karon farko ake nuna su a duniya, ko a nahiyar Asiya ko kuma a kasar Sin, a wajen bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko kuma CIIE karo na biyar.
Kididdigar ta nuna cewa, yawan sabbin kayayyaki, da fasahohi, da kuma hidimomin da aka nuna su ya zarce 1500, a wajen bukukuwan CIIE hudun da suka gabata.
A wajen bikin na bana, za’a gudanar da bukukuwan nuna sabbin kayayyaki guda 94, inda za’a fitar da sabbin kayayyaki sama da 170.
Ina dalilin da ya sa aka kara samun sabbin kayayyaki da fasahohi da hidimomi a wajen bikin CIIE?
Kasar Sin na da mutanen da yawansu ya kai biliyan 1.4, ciki har da masu samun matsakaicin kudin shiga fiye da miliyan 400. A shekaru biyar, kamfanoinn kasa da kasa sun maida babbar kasuwar kasar Sin a matsayin wuri mafi kyau gare su, na fitar da sabbin kayayyaki da fasahohi da hidimomi.
Yin kirkire-kirkire zai samar da makoma mai haske. Duk wani sabon abun da za’a fito da shi a wajen bikin CIIE, zai wakilci wani sabon zarafin kasuwanci, ko kuma wani sabon karfin yin kere-kere, ko kuma wani sabon salon rayuwa.
Mutane suna kara maida hankali kan sabbin kayayyaki, da fasahohi da hidimomi, al’amarin da ba damammakin hadin-gwiwa kawai ya samar ba, har ma da makoma mai haske. (Murtala Zhang)