Motoci akalla 20 ne suka kone a lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka kutsa cikin wata harabar kungiyar agaji da ke garin Monguno da ke arewacin Jihar Borno.
An tattaro cewar masu tada kayar baya na kungiyar IS da ke samun goyon bayan ISWAP sun kai hari garin da misalin karfe 1 na daren ranar Alhamis, inda suka rika harbe-harbe.
- Kasar Sin Ta Kasance Ta Farko Wajen Yawaitar Mutane Masu Hazaka A Duniya
- Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Kano – FRSC
Wani rahoton sirri da aka samu daga majiyoyin tsaro na Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya tabbatar da cewa maharan sun afkawa ma’aikatan agaji.
Majiyar ta ce bayan da suka kasa gano ko mutum daya daga cikin ma’aikatan da ke cikin harabar, sai suka kone motoci 18 tare da lalata wasu guda biyu.
‘Yan ta’addan sun kuma yi yunkurin kwashe motoci kirar 4X4 hilux guda uku amma sun gamu da fushin rundunar sojojin Operation Hadin Kai, inda suka yi musu ruwan wuta.
A cewar majiyar, ‘yan ta’addan sun yi musayar wuta da jami’an tsaro, inda aka yi dauki ba dadi.
Sai dai ba a samu asarar rai ba a yayin harin.
Monguno yana kusa da yankin tafkin Chadi a Nijeriya.
ISWAP ta sha kai hari garin a lokuta da dama.