Kimanin sati uku zuwa hudu kenan, al’ummar yankin Hayin gado da ke gundumar Kusharki ta karamar hukumar Rafi ke cikin zullumi da fargabar rashin ‘ya’yansu sakamakon garkuwa da su da ‘yan ta’adda suka yi.
Kusharki wadda ke cikin karamar hukumar Rafi tana kan iyaka ne da karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, kuma tana daya daga cikin gundumomin da ‘yan ta’adda suka hana wa natsuwa da kwanciyar hankali, saboda yawan hare-haren.
Shugaban matasan yankin Hayin Gado, Malam Awal Barau ya ce, “Maganar gaskiya muna cikin tashin hankali a yankin nan, yanzu idan ka lura jama’a sun watse, wanda saboda albarkar kasar noman da ke yankin nan rani da damuna ba ka rasa mu da jama’a, amma mun zama ‘yan tsiraru.
“Sati na uku zuwa hudu kenan ‘yan ta’addan suka kwashe mana yara a gona sun tafi tsigar gyada kuma har zuwa yanzu ba wanda aka sako. Yaran duk masu karancin shekaru ne, mata sha shida ne, sannan maza hudu ba mu da wani labari yanzu haka a kansu.
“Abin da ke daure mana kai, a baya an ba mu jami’an tsaro wanda suke bakin kokarinsu a kowani lokaci, yanzu muna neman masu ruwa da tsaki a cikin gwamnati da su sanya baki wajen ganin an kubutar da yaran nan.
“Muna da hakki ga gwamnati kamar yadda take da hakki a kanmu, hakkinmu kare muna rayuka da samun walwala.
Mu a Kusharki gaskiya ba mu da shi. Idan ka ga sun shigo sai lokacin zabe tare da jami’an tsaronsu. Ya kamata shugabanni su ji tsoron Allah su kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’a.