Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-ruf’i, ya tabbatar da maigirma Wazirin Jere a matsayin sabon Sarkin Jere.
Wazirin Jere, Alh. Abdullahi Daniya, wanda shi ne ke rike da masarautar ta jere na tsawon shekaru takwas tun bayan Jinyar marigayi Mai martaba Sarkin Jere, Dr. Sa’ad Usman OFR, har zuwa wannan rana.
- Shugaba Buhari Ya Karrama CGI Isah Jere Da Lambar Yabo Ta Ƙasa Bisa Mutunta Ɗan’adam A Shugabancinsa
- Mun Duƙufa Tabbatar Da Tsaron Iyakokin Nijeriya – CGI Isah Jere
Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da nadin Wazirin Jere, Alh. Abdullahi Daniya a matsayin wanda zai maye gurbin marigayi Dr. Sa’ad Usman.
Mun samu sanarwar tabbatar da nadin sabon Sarkin naa Jere daga Jami’in watsa labarai na masarautar, Ahmad Abdulkarim Dalhat, a ranar Juma’a, 11 ga Nuwambar 2022.