Zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Zhang Jun, ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa, da su kara ba da taimako ga kasashen Afirka don kara kwarewarsu a fannin yakar ta’addanci, ta yadda za a kawar da matsalar daga tushe.
Jami’in Sin ya furta haka ne a taron manyan jami’an yaki da matsalar ta’addanci a nahiyar Afirka na kwamitin sulhu na MDD, inda ya shawarci kasashe daban daban, da su taimakawa kasashen Afirka karfafa bangarori masu rauni, da ba da karin tallafi na kudade, da kayayyaki, da bayanai da dai sauransu.
Jami’in ya kuma nanata cewa, ya kamata a girmama ’yancin kasashe, da bangarorin ketare dake hadin gwiwa da kasashen Afirka, yayin da ake hadin kai da su wajen tinkarar matsalar ta’addanci, kana a daina gindaya musu wasu sharudda da suka shafi batun siyasa.
Zhang Jun ya kara da cewa, ya kamata MDD ta kara mai da hankali kan ra’ayoyin kasashen Afirka, da bukatunsu na raya kasa, da kokarin samar musu da yanayi mai kyau da zai taimaka musu wajen cimma burin da suke fatan cimmawa.
A cewar jami’in, a ko da yaushe kasar Sin ta kasance mai nuna goyon baya ga kasashen Afirka, wadda kuma ke samar musu da gudunmawa ga kokarinsu na tabbatar da kwanciyar hankali. Kasar Sin za ta ci gaba da hada kai tare da gamayyar kasa da kasa, wajen samar da karin taimako ga kasashen Afirka, don ganin an tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a nahiyar. (Bello Wang)