A daidai lokacin da ake kara kusantar babban zaben 2023, a ranar Asabar wata majiyarmu ta nakalto cewa wasu shugabannin Arewa sun fara yunkurin ganin an samu daidaito wajen tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya tilo daga yanki.
Majiyar ta shaida cewar shugabannin da dama a Arewa suna fatan cewa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da ya zama dan takarar shugaban kasa daya tilau da zai fito a dama da shi a zaben 2023.
- Gwamnan Bauchi Ya Amince Da Fitar Da Miliyan 500 Don Biyan Giratuti
- Mutane 11 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Kogi
Hakan kai tsaye na kara fito da yadda ake yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso matsin lamba da ya amince ya mara wa Atiku baya domin yankin ta zama tana da dan takara guda.
“Mutanenmu sun cimma matsayar fitar da dan takara guda a zaben 2023 kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar aka zaba na jam’iyyar PDP,” a cewar majiya da ta bukaci a sakaya sunanta.
A cewar majiyar hakan zai taimaka sosai wajen ganin Arewa ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2023 da ke tafe, inda suka ce sun yi amannar muddin Atiku da Kwankwaso suka hada kai yankin zai iya lashen zaben.
Majiyar wadda wani fitacce ne cikin kungiyar dattawan Arewa ya kara da cewa jigogi da daman gaske daga Arewa na kara matsa lamba wa dan takarar NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da ya janye ya kuma mara wa Atiku baya.
“Ina mai tabbatar maka cewa shugabanninmu a Arewa suna kan matsa lamba wa Kwankwaso da ya janye neman takararsa ga Atiku domin cigaban jama’anmu da yankinmu,” a cewar majiyar.
Sai dai kuma duk da hakan, tawagar Kwankwaso dai sun nuna cewa tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi biris da wannan matsin lambar da ake masa inda ya kara azama da burin cimma manufar da ya sanya a gaba.
Sai dai kuma karashin amincewar Kwankwaso na ya amince da wannan kokarin Bai rasa nasaba da dalilan da suka sanya shi fita daga cikin jam’iyyar PDP a baya.
“Zai yi matukar wahala Madugu ya mara wa PDP baya bisa yadda wasu makusantan Atiku ke bi da shi lokacin da yake tare da su, gaskiya dai da kamar wuya.”