Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Asabar ya sake bude babbar kasuwar Shanu ta kasa da kasa ta Gamboru wanda aka rufe sama da shekaru bakwai sakamakon hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar.
Babbar kasuwar wacce take da matsuguni a Gamboru, waje ne da ake gudanar da harkokin kasuwanci sosai a iyakar karamar hukumar Ngala da ke cikin tsakiyar jihar Borno.
- Zulum Ya Bai Wa Matasan Biu 1,000 Tallafin Miliyan 100 Don Yin Jari
- Zulum Ya Shigar Da Marayu 7000 Makaranta A i
Gamboru ta hada iyaka da Jamhuryar Kamaru kuma hanyarta na iya hadawa zuwa N’Djamena babban birnin jamhuriyyar Chad.
Zulum wanda ya kasance a karamar hukumar ta Ngala na tsawon kwanaki biyu domin gudanar da harkokin da suka shafi jin kai, ya sake bude kasuwar ne da rakiyar babban jami’in da ke bada umarni (CO) na bataliyar soji ta 3, Lt. Col. Tolu Adedokun, tare da shugaban karamar hukumar Hon. Mala Tijjani.
Zulum ya jinjina da irin kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da rundunar sojin kasa, ‘yan sanda, hukumar tsaron farin kaya, da sauran bangarorin tsaro ciki har da na masu sa-kai da suka bada tasu gudunmawar wajen tabbatar da dawo da tsaro da zaman lafiya a jihar Borno, wanda hakan ne ya kai ga samun nasarar sake bude kasuwar.
Daga nan sai ya yi gargadin cewa, duk wani ko wasu dillalan shanu da aka sake kamawa da shiga cikin harkokin ta’addanci, lallai hukuma za ta dandana masa kudarsa.
Kwamishinan matasa, wasanni da yaki da fatara na jihar, Saina Buba, wanda ya jagoranci kwamitin kula da harkokin shanu a jihar, ya yi bayanin cewa a kalla duk rana ana jigilar shanu sama da 500 ko 800 zuwa kasashen makwafta daga wannan kasuwar.
A cewarsa, dubban mutane ke amfana da kasuwar ta hanyar samar musu da ayyukan yi, da kuma bunkasa harkokin kasuwanci.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar shanu ta jihar, Alhaji Yakuba Goni, ya gode wa gwamnan bisa sake bude kasuwar tare da shan alwashin cewa za su taimaka wajen kyautata lamura.