Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki, a ranar Litinin ya nuna kwarin guiwarsa na cewa rashin jituwar siyasa da ke tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da tawagar gwamnonin G-5 da ke karkashin gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, zai zama tarihi domin kuwa kwanan nan za a shawo kansa.
Saraki wanda ke magana da ‘yan jarida a Illorin ta jihar Kwara yayin addu’o’in tunawa da mahaifinsa karo na 10, marigayi Dakta Abubakar Olusola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa a zamanin Jamhuriyar ta biyu.
- Rikicin Cikin Gidan APC Da PDP: Shin ‘Yan Jihar Ribas Kadai Aka Bata Wa Rai?
- Rikicin PDP: Ina Farin Ciki Da Sulhun Da Rundunar Wike Ta Nemi A Yi – Atiku
Da ya ke amsa wa manema labarai tambayoyinsu kan rikicin cikin gida na PDP, Saraki ya ce, “Za mu bai wa ‘yan Nijeriya mamaki. Za mu yi aikin hadin guiwa dukkaninmu domin tabbatar da an inganta Nijeriya.
“Tabbas ina sake nanatawa za mu bai wa al’umar Nijeriya mamaki. Saboda dukkaninmu mun hadu ne a turba guda ta yadda za a inganta wannan kasar.
“Za mu jingine komai mu sanya ‘yan Nijeriya a tunaninmu na farko saboda muna da buri da son PDP ta dawo mulki.