Kotun Daukaka da ke Sakkwato ta tabbatar da Sani Yakubu Noma a matsayin dan takara a kujerar Majalisar Wakilai a Mazabar Tarayya ta Argungu/Augie da ke a Jihar Kebbi ta hanyar tabbatar da hukuncin Kotun Tarayya da ke a Kebbi.
Jagoran lauyoyi uku, Mai Shari’a M. L Shu’aibu wanda ya karanta hukuncin ya bayyana cewar kotun ta yi watsi da karar Haruna Garba saboda Noma ne ya samu nasarar lashe zaben fitar da gwanin takarar jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 5 ga Satumba 2022.
- Rikicin PDP: Ina Farin Ciki Da Sulhun Da Rundunar Wike Ta Nemi A Yi – Atiku
- Bagudu Ya Amince Da Nadin Sarakunan Gargajiya 2 A Masarautar Yauri Ta Jihar Kebbi
A hukuncin wanda sauran alkalan kotun biyu, Moses Ogu da Muhammad Idris, suka yi na’am da shi, ya bayyana cewar Noma ne halastaccen dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023 don haka canza shi da aka yi kuskure ne.
Haruna Garba, tsohon Shugaban Hukumar KEDCO, ya shiga zaben fitar da gwanin takarar Gwamna amma bai samu nasara ba, haka ma ba ya cikin wadanda suka shiga zaben Mazabar Tarayya ta Argungu/Augie amma a Hukumar Zabe aka canza sunan Noma da ya yi nasara da wanda hakan kuskure ne in ji kotun.
A zantawar Noma wanda ya yi karar jam’iyyarsa ta PDP da Hukumar Zabe kan canza sunansa da aka yi, ya bayyanawa manema labarai cewar kotun ta yi hukuncin gaskiya da adalci tare da godewa kotun a kan tabbatar masa da gaskiya da ta yi.