Kamfanin Amazon na shirin sallamar kusan ma’aikata 10,000, kamar yadda jaridar New York Times ta rawaito a ranar Litinin.
Wannan zai wakilci kasa da kashi daya cikin dari na jimmilar albashin kamfanin wanda ke da ma’aikata miliyan 1.54 a duk fadin duniya a karshen watan Satumba.
- Ganduje Ya Ware Naira Miliyan 300 A Matsayin Kudin Karatun Daliban Kano Da Ke Karatu A Waje
- Halartar Manyan Kamfanonin Kasa Da Kasa A Fannin Chips Bikin CIIE Ta Nuna Aniyarsu Ta Rungumar Kasuwar Kasar Sin
Rahoton Times ya ce wuraren da abin ya shafa sun hada da sashen na’urori na Amazon, tallace-tallace da albarkatun dan adam.
Ma’aikatan da aka kora za su fuskanci tashin hankali biyo bayan sallamarsu daga aiki.
Biyo bayan tabarbarewar tattalin arziki, makonni biyu da suka gabata Amazon ya ba da sanarwar dakatar da daukar ma’aikata kuma tuni ma’aikatansa suka ragu idan aka kwatanta da farkon shekara.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya tuntubi Amazon, amma ba a samu jin ta bakin kamfanin ba.