Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce a shirye Sin take, ta ci gaba da hada gwiwa da kasashe mambobin kungiyar G20, wajen gina tsarin tattalin azikin duniya na zamani, wanda zai kasance dunkulalle, bisa daidaito da hadin gwiwa da moriyar juna da ci gaba na bai daya da kowa zai mora.
Xi Jinping ya bayyana haka ne a yau Laraba, yayin da yake jawabi ga taron kolin G20 karo na 17 a tsibirin Bali, na kasar Indonesia.
Da ake tattaunawa game da komawa amfani da fasahohin zamani, shugaba Xi ya ce fadada tattalin arziki irin na zamani da hanzarta komawa amfani da fasahohin zamani, sun zamo muhimman batutuwan dake tasiri kan tsarin tattalin arzikin duniya.
Yayin taron G20 da aka yi a Hangzhou a shekarar 2016, a karon farko, kasar Sin ta sanya batun tattalin arziki na zamani cikin ajandar taron, inda ta lashi takobin kirkiro hanyoyin samun ci gaba tare da lalubo damarmakin ci gaba dake akwai.
Shugaban na Sin ya ce kamata ya yi a bayar da fifiko ga samun ci gaba, inda ya ce wajibi ne a cike gibin fasahohin zamani dake akwai, haka kuma kirkire-kirkire ya zama jigon ingiza ci gaba, bayan shawo kan annobar COVID-19. (Fa’iza Mustapha)