Birgediya-Janar Audu Ogbole James, daraktan kudi a cibiyar kula da matsugunan sojojin Nijeriya (NAFRC), Oshodi, Legas, ya rasu.
Janar din ya rasu ne bayan wani kofur mai suna Abayomi Edun ya buge shi da mota a barikin a ranar Talata da daddare.
An bayyana cewa marigayin yana tafiya zuwa gidansa ne inda kofur din ke tuka wata mota kirar SUV mai lamba EKY 177 FX, nan ajali ya faru.
Talla
An bayyana cewa, kofur Edun a make yake da barasa a lokacin da hatsarin ya afku.
Wata majiya ta shaida wa kamfanin Daily trust cewa, an garzaya da marigayin zuwa cibiyar kula da lafiya ta NAFRC inda kuma likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Talla