Sanata Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya yi watsi da zargin da ake masa na cewa bai damu da kiristoci.
Zaben Sanata Kashim Shettima da Tinubu ya yi a matsayin mataimakin sa a zaben shugaban kasa a 2023, ya haifar da cece-kuce daban-daban.
A wani zaman tattaunawa da shugabannin kungiyar Kiristocin Nijeriya CAN, Tinubu ya yi watsi da wadanda suka bayyana shi a matsayin mai kishin addininsa kadai, inda ya ce zabin Shettima ba shi da alaka da addini.
Ya ce ba shi da wani abu da zai sa yaki addinin Kiristanci, hasali ma, matarsa da ’ya’yansa shine addinin da suka yi imani da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp