Dan majalisar dokokin Jihar Legas, Hon. Abdulsobur Olayiwola Olawale ya rasu a wajen kaddamar da takarar Tinubu a Jos, babban birnin Jihar Filato.
Marigayin na wakiltar mazabar Mushin II a majisar dokoki Jihar Legas.
- Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Afirka Ta Kudu Da Na Kasar Senegal
- Sufeton ‘Yansanda Ya Ba Da Umarnin Tsaurara Tsaro A Hanyar Legas-Ibadan
Rahotanni sun ce jigon jam’iyyar APC ya mutu a filin wasa na Rawang Pam Township da ke Jos.
Talla
A ranar Talata ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya kaddamar da yakin neman zabensa na 2023 a Jihar Filato.
Omititi ya kasance shugaban kwamitin majalisar akan ayyuka na kananan hukumomi.
An nada marigayi dan majalisar a matsayin Sariki Adeen na babban masallacin Mushin a shekarar 2017.
Talla