• English
  • Business News
Friday, October 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Ya Yi Kira Da Dunkule Tattalin Arzikin Asia Da Pasifik Yayin Da Ake Fuskantar Kalubale

by CMG Hausa
3 years ago
Xi

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya bayyana a yau Alhamis cewa, yayin da ake fuskantar sabbin sauye-sauye, akwai bukatar mambobin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin Asiya da Pasifik wato APEC, su yi waiwaye su dauki darasi daga tarihi, su tunkari kalubalen da ake fuskanta yanzu, tare da jajircewa wajen dunkule tattalin arzikin yankin Asia da Pasifik.

Xi Jinping wanda ya bayyana haka cikin rubutaccen jawabin ga taron kolin shugabannin masana’antu da kasuwanci na kungiyar APEC, ya yi kira da a hada hannu wajen samar da sabbin nasarori a fannin ci gaba da gina al’ummar Asia da Pasifik mai makoma ta bai daya.

  • Xi Jinping Ya Gana Da Babban Sakataren MDD

Ya kuma gabatar da wasu shawarwari 6 game da hakan, wadanda suka hada da, gina tubalin neman ci gaba cikin lumana da daukar dabarun neman ci gaba dake mayar da hankali kan moriyar jama’a da fadada bude kofa ga kasashen waje da jajircewa wajen hadewa da juna da gina nagartaccen tsarin samar da kayayyaki da kuma daukaka aikin raya tattalin arziki.

A cewar shugaba Xi, yankin Asiya da Pasifik ba wuri ne da kowa zai yi abun da ya ga dama ba, kuma bai kamata ya zamo dandalin takara ga manyan kasashe ba. Yana mai cewa, ba za a amince da duk wani yunkuri na tayar da wani yakin cacar baka a yankin ba.

Har ila yau, shugaban na kasar Sin ya bayyana cewa, bin tafarkin neman ci gaba cikin lumana, muhimmin zabi ne da kasarsa ta yi saboda muradun al’ummar Sinawa, kuma za su jajirce ga tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba da hadin gwiwa da samun moriyar juna.

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Haka kuma, za su mayar da hankali ga kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya, yayin da suke neman na su ci gaban, kana za su bayar da karin gudunmuwa ga zaman lafiyar duniya da ci gaba, ta hanyar na su ci gaban.

Da yake bayyana bude kofa da dunkulewa wuri guda a matsayin masu muhimmanci ga kwanciyar hankali da ci gaban bil Adama, Xi Jinping ya ce, daukacin al’ummar Asiya da Pasifik ne suka raya yankin ta hanyar hada hannu da shawo kan wahalhalu da kalubale.

Yana mai cewa, duk wani yunkuri na kawo tsaiko ko rusa tsarin samar da kayayyaki, da aka samar a yankin cikin shekaru da dama, babu abun da zai haifar face lalata hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin.

Ya ce bude kofa zai kawo ci gaba, yayin da rufewa za ta haifar da koma-baya. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

October 31, 2025
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

October 31, 2025
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

October 30, 2025
Next Post
Sake Fasalin Naira: Adadin Gwamnonin Da EFCC Ke Bibiya Na Sake Karuwa –Bawa

Sake Fasalin Naira: Adadin Gwamnonin Da EFCC Ke Bibiya Na Sake Karuwa –Bawa

LABARAI MASU NASABA

Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede

Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede

October 31, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida

October 31, 2025
Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

October 31, 2025
Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa

October 31, 2025

Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda

October 31, 2025
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai

October 31, 2025
Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.