• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Ba Da Gudunmawar Ci Gaban Duniya

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Abokai, yayin da ‘yan kwanaki suka rage a fara gasar cin kofin kwallon kafan duniya ta hukumar FIFA ta 2022 a Qatar, yau “duniya a zanen MINA” zai bayyana muku abubuwan dake da alaka da kasar Sin a wannan gasa da ma duniya.

Yayin da ka yi yawo a wajen filin wasa na Al Bayt , abin da zai shakatar da kai a filin, shi ne wasu bishiyoyi masu kyaun gani na kudancin kasar Sin da yawansu ya kai fiye da dubu 50, da kamfanin samar da tsirrai na birnin Foshan na lardin Guangdong dake kudancin Sin ya yi jigilarsu zuwa wurin.

  • Masana: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Karfin Afirka A Fannin Aikin Injiniya

Ban da wannan kuma, sama da kashi 50% na kayayyakin dake da alaka da gasar daga birnin Yiwu na Sin ne aka samar, baya ga rigunan wasa na fitattun kungiyoyin ‘yan wasa na kasashe 32 da mai tsara salon tufa na Sin ya gabatar da mutum zai iya saya.

Haka kuma, kamfanin Sin ne ya gina filin wasa na Lusail, daya daga cikin filaye mafiya kayatarwa da muhimmanci na gasar.
Bayan ga wadannan abubuwa da Sin ta samar a gasar, yanzu haka kayayyakin da Sin ta samar da manyan ababen more rayuwa da Sin ta gina sun karade sassa na duniya. Idan muka juya ga nahiyar Afrika kuwa, daga layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya zuwa layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna, daga madatsar ruwa ta Merowe zuwa tashar jirgin ruwa mai zurfi ta Lekki ta ciniki cikin ‘yanci, da ma wasu abubuwa na yau da kullum, dukkansu Sin ce ta gina su.

Tambayar ita ce, wai me ya sa kasar Sin ta gina wadannan abubuwa masu tarin yawa a duniya?
Bayan shekaru fiye da 40 da Sin ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, Sin ta zama kasa mai karfi a fannin masana’antu a duniya. Ban da wannan kuma, a cikin tsarin zamanintar da masana’antu da Sin ta gudanar, gwamnati ta mai da hankali matuka kan kimiyya da fasaha.

LABARAI MASU NASABA

Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji 

Alal misali, layin dogo da kamfanin Sin ya shimfida a cikin Abuja, shi ne irinsa na farko a yammancin Afrika dake amfani da tsarin kasar Sin. Ban da wannan kuma, fasahar sadarwa ta 5G da manyan ababen dangane da hakan da ake amfani da su yanzu a Afrika, su ma kamfanonin Sin suka gina su.

Sanin kowa ne cewa, ana yabawa kayayyakin da Sin ta samar saboda inganci da kuma araha, baya ga haka, abubuwan da Sin ta samar ta hanyar kirkire-kirkire bisa fasaha da kimiyya, sun fara jawo hankalin duniya.

Kasashe daban-daban na sa ran shigo da kayayyakin Sin cikin kasashensu da kuma hada kai da kamfanonin Sin a fannin samar da kayayyaki da fasaha da kimiyya, kazalika suna zabar kamfanonin Sin, don su taimaka musu wajen gina wasu manyan ababen more rayuwa.

A nata bangare, Sin tana matukar fari ciki wajen hada kai da kasashen duniya musamman ma kasashe masu tasowa don samun moriya tare.(Mai zane da rubuta:MINA)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan
Daga Birnin Sin

Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

October 15, 2025
Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji 
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji 

October 15, 2025
Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia
Daga Birnin Sin

Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia

October 15, 2025
Next Post
Peng Liyuan Ta Gana Da Uwar Gidan Shugaban Indonesia

Peng Liyuan Ta Gana Da Uwar Gidan Shugaban Indonesia

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato

An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato

October 16, 2025
Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

October 16, 2025
Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

October 15, 2025
Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari 

Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari 

October 15, 2025
Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji 

Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji 

October 15, 2025
Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano

Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano

October 15, 2025
Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar

Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar

October 15, 2025
Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia

Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia

October 15, 2025
Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya 

Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya 

October 15, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.