Kamfanin jaridar LEADERSHIP ya sanar da wadanda suka samu nasara zama gwaraza a bangarori da daban-daban dama na rayuwa a wannan shekarar ta 2022. Bikin karrama ‘yan Nijeriya da suka yi fice na LEADERSHKIP na daya daga cikin bukuwan karramawa da ya fi shahara a Nijeriya.
Wadanda suka samu nasarar zama Gwarazan ‘yan Nijeriya na kamfanin Leaderhip su uku sun hada da Shugabban Bankin Afredim Bank, Farfesa Benedict Oramah; Shugaban Hukumar Yaki Da Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai Ritaya); da kuma shaharrariyar ‘yar wasan guje-guje na duniya, Oluwatobiloba Ayomide Amusan.
Sanarwa da ta fito daga mahukuntan kamfanin ya kara da cewa, “Kamar yadda muka saba a duk shekara, muna sanar da sunayen wadanda suka lashe lambar karramawar na bangarori daban-daban, wannan kuma yana faruwa ne bayan aikin tantancewa yadda yakamata, muna fatan jerin sunayen wadanda suka yi nasarar a dukkan bangarorin zai zaburar da al’umma duk kuwa da kalubalen da muke fuskanta a matsayin kasa.”
A rukunin Gwarzon LEADERSHIP na 2022, Farfesa Oramah tare da wasu mutum biyu suka samu nasarar lashewa, saboda manya-manyan gudummawarsa da nasarorin da ya samu a sassan duniya, wanda haka ya sa ya yi fice a matsayin wani wakili na musamman ga Nijeriya da duniya baki daya.
Shugaban hukunmar NDLEA, Marwa, wanda a halin yanzu ya zama tashin hankali da barazana ga garwurtattun masu safarar kwayoyi a Nijeriya, ya samu nasarar zama Gwarzon LEADERSHIP na shekara tare da Farfesa Oramah saboda nasarorinsa a yaki da safara tare da shan miyagun kwayoyi musamman a kan yadda ya sammu nasarar tarwatsa gungun masu safarar muggan kwayoyi tare da kuma sake fasalin hukumar ta yadda a halin yanzu tana gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Shahararriyar ‘yar wasan tsalle-tsalle na duniya, Amusan, ita ma ta samu nasara a kan bajintar da Gail Debers ya yi shekara 22 da suka wuce ta kuma kare wannan nasarar a gasar Diamond League a bangaren tsallke shinge na mita 100, wadannan na daga cikin nasarorin da ta samu a shekarar 2022, nasarar da ta samu a cikin dakika 12.29.
“A wanann rukunin ya zama dole a karrama wadanda suka yi fice a tare aiki tukuru wajen tasiri a rayuwarmu gaba daya, muna kuma ganin wannan zai cigaba da zaburar da al’unmmar kasa baki daya,” in ji hukumar gudanarwar.
Haka kuma a shekarar 2022, gwamnonin jihohi uku suka samu nasarar zama Gwarazan Gwamna na LEADERSHIP na shekarar 2022. Sune kuma Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna; Prince Dapo Abiodun na JIhar Ogun; da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Inugu.
An ba wadannan gwamnonin wannan kyautar ne saboda ayyukan da suka gudanar a jihohinsu da ya kai ga bunkasa rayuwar al’ummar jihohin nasu da kuma yadda suke gudanar da safarar kudaden jihar a bayyane ba tare da munamuna ba haka kuma da yadda suka rungumi bunkasa samar da kayyakin more rayuwar al’ummarsu da samar da hanyoyin kasuwanci ga mutanesu.”
Gwamna El-Rufai, wanda aka bayar da sunansa a shekarar data wuce, sun hadu a nasarar zama Gwarazan Gwamna na Leadership ne, musamman a kan kokarinsa na bunkasa Jihar Kaduna ta hanyar samar da karkarfar tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da kuma sake fasalin tsarin aikin gwamnati ta hanyar tsuketa da kuma zaburar da ita don biyan bukata.
Haka kuma Gwamna Abiodun ya samu nasarar zama Gwarzon Gwamna ne saboda yadda ya tsayu wajen samar wa al’ummar Jiharsa ababen more rayuwa da kuma fadada harkokin kasuwanci ga al’ummar jihar baki daya.
Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya samu zama Gwarzon Gwamna na shekarar 2022 a bisa kokarinsa na dora jihar a hanyar tsayuwa da kafarta a bangaren tattalih arziki da kuma samar ababen more rayuwa a sassa jihar duk kuwa da matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankin.
A wani bangare na wadanda za a karrama d, lambar Gwarzon Dan Siyasa na 2022 an mika ta ne ga Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda harkokin siyasarsa ta shiga zuciyar al’umma kasa tun bayan da aka kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a watan Mayu, shi kadai ne ya samu wannan nasarar a wannan rukunin.
Lambar Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati na LEADERSHIP na 2022 ya tafi ne ga Shugaban Hukumar tara Kudaden Haraji na Kasa, (FIRS), Muhammad Mamman Nami; da Shugaban Hukumar Gidauniyar Horas da Dalibai, (ITF), Joseph Ari, da kuma shugaban Huukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS), Jere Idris.
LUTUS Bank ce ta lashe lambar Gwarzon Banki na shekara saboda yadda Banki ya fuskanci samar kirkire-kirkire a harkokinsa wanda hakan ya kara wa bankin mutunci kwarai da gaske; lambar Gwarzon Inganta walwala na LEADERSHIP ya shiga hannun mutum biyu ne, da shugabar gidan marayu na ‘Needy Foundation’, Fasto Solomon Folorunsho, saboda kokarinsa na tallafa wa al’umma duk kuwa da karancin kudaden da gidauniyar ke fuskanta da kuma wanda ya kirkiro ‘Chess In Slums Africa’, Tunde Onakoya.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, dan asalin Jihar Borno, Injiniya Mustapha Abubakar Gajibo ya lashe lambar Gwarzon kikira a fagen kare muhalli na shekarar saboda samar da mota mau amfani da lantarki.
Shugabar Bankin Fidelity Bank Plc, Misis. Nneka Onyealu-Ikpe, ta lashe lambar Gwarzuwar Ma’aikaciyar Banki na shekarar 2022 saboda kokarinta na tallafa wa kananan masana’antu da samar musu ta kudade cikin sauki, yayin da lambar Gwarzuwar ‘Yar Kasuwa na LEADERRSHIP ya tafi ga shugabar Kamfanin ‘Mojec International Holdings’, Misis. Chantelle Abdul.
Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta samu nasarar zama Gwarzuwar Hukumar Gwamnati na shekarar 2022 saboda kokarin da hukumar ta yi a cikin shekara daya da ta wuce.
Sauran wadanda suka samu nasarar sun hada da Gwarzon Kamfani na shekara, wanda Kamfanin ‘Bua Foods’ ya samu lambar Gwarzon kamfanin da yake aiki da hanyoyi na zamani, sai kuma ‘Coleman Cable and Wire’; da kuma Gwarzon kamfanin sadarwa na shekara wanda ‘MTN Nigeria’ ta lashe, saboda yadda ta yi tsayin daka wajen gudanar da ayyuukanta.
Kamfanin shinkafa na Mama Pride ya lashe lambar kayan da aka kirkira na zamani a wannan shekarar, don ta zama ana ganinta a ko ina a kasar nan.
Gwarzon shugaban kamfani na shekara kuma, shugaban bankin Zenith, Ebenezer Onyeagwu, ya samu wannan kyautar saboda jajjircewarsa wajen bunkasa bankin.
Wanda ya samu lambar karramawa ta Gwarzon mai amfani da kayan gida a bangaren Albarkatun Mai shi ne shugaban Hukumar Kula da yadda ake gabatar da shirin gudanar da bunkasar bangaren Mai da hannun al’ummar gida, Mista Simbi Wabote; yayin da Gwarzon Kamfanin da ya ke gudanar da kasuwanci na intanet shi ne “Pocket Money”.
Wanda ya lashe Gwarzon Mawaki na LEADRESHIP a wannan shekafrar shi ne ’Afro Pop RnB hip-hop music rabe’ ‘Buga crooner’, Kiss Daniel.
Gwarzon dan wasan Leadership na wannan shekarar ya tafi ne ga kungiyar kwallon kafa ta mata ‘yan kasa da shekara -17 wanda suka buga gasar FIFA sun kuma samu nasararori da dama a wasannin da aka yi a tsakanin 5-24 ga watan Agusta a Rio de Janeiro ta kasar Brazil; yayin da dan shekara 13 dan makarantar Firamare daga jihar Borno, Musa Sani, wanda ya zama gadar sama da kasa ya lashe bangaren Gwarzon Yaro na shekarar 2022.
Sanarwa ta kuma bayyana cewa, dukkan wadanda aka ayyana za a karranma su ne a babban taron Leadership da za a yi a cikin shekara mai zuwa a wata ranar da za a sanar a nan gaba