Rahotanni sun tabbatar cewa adadin tubabbun mayakan Boko Haram, wadanda suka ajiye makaman su tare da mika wuya ga sojoji, a karkashin shirin yiwa mayakan afuwa; wanda yanzu haka adadin tubabbun mayakan, al’amarin da yake ci gaba da fuskantar kalubale kala-kala, kama daga rashin gamsuwa, karanci tanadin da ya dace a samarwa shirin karbar tubabbun, sannan da rashin samun isasshen lokacin tattaunawa da jama’ar da abin ya shafa kai tsaye.
Mista Chris Musa, shi ne Babban Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai, mai yaki da masu tayar da kayar baya a Arewa Maso Gabas, ya ce adadin yan ta’addan Boko Haram wadanda a suka mika wuya ga sojojin su ya doshi 80,000, tare da bayyana cewa suna aiki da gwamnatin Borno domin kula da tsoffin yan ta’addan, a sansanoni uku dake jihar Borno.
- Ana Baje Kolin Shirye-Shiryen CMG A Taron Kafofin Watsa Labaran Kasa Da Kasa Karo Na Farko
- 2023: Wike Zai Goyi Bayan Peter Obi Ya Yi Watsi Da Takarar Atiku
Ko a cikin watan Fabrairun da ya gabata, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya na bayyana cewa sama da kashi 90 cikin dari na tuban Boko Haram gaskiya ne. Sanarwar da tayi hannun riga da wadda Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna, a watan Disamban shekarar da ta gabata, inda ya ce bai yarda da gyara halayyar yan ta’adda ba, wanda shima Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Lawan ya bukaci ayi kaffa-kaffa kan batun.
Zulum ya bayyana hakan ne a sa’ilin da yake amsa tambayoyi daga manema labaru, jim kadan da kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan dawo da yan gudun hijirar Arewa Maso Gabas garuruwan su, ya ce tuban da yan ta’addan Boko Haram suka yi tare da mika wuya gaskiya ne.
Ya ce, “Na yi imanin, sama da kashi 90 cikin 100 na wadanda suka mika wuya, yana da kyau kuma suna taimaka wa gwamnati ta yadda ya dace; saboda yadda suke kiran abokan aikinsu a cikin daji su fito su shiga aikin samar da zaman lafiya.”
Tun bayan bullo da shirin yiwa mayakan afuwa, sarakunan gargajiya tare da shugabannin addini a jihar Borno sun nuna cewa abu ne mai wuya al’ummar jihar su karbi tuban Boko Haram.
Da yake magana kan batun a watan Agustan shekarar da ta gabata, Shehun Borno, Alhaji Abubakar El-Kanemi, ya ce wannan shiri ci gaba ne wanda za a yi marhabin da shi, amma jama’a za su ci gaba da tuna mummunan ta’addancin da tubabbun Boko Haram suka aiwatar wa jama’ar jihar na tsawon shekaru 12.
“Haka kuma, wannan shiri na “Safe Corridor” wanda Sojoji suka bullo dashi ya taimaka wajen dakile ta’addanci tare da tilastawa wasunsu ajiye makamai da yin tuba. Amma abu ne mai matukar wuya ace mu zauna da tubabbun yan ta’addan a garuruwan mu da suka kona.”
Wasu rahotanni sun nuna yadda maharan sun kashe hakimai 13 a jihar Borno. Al’amarin da Shehun Borno ya bayyana da cewa, “Abu ne mai sauki a yafe asarar rayuka da dukiyoyin, amma da wuya mu manta da asarar rayukan da aka yi cikin wadannan shekaru 12.”
A wani zama na daban da Gwamnan jihar Borno ya jagoranta na masu ruwa da tsaki a jihar, sun amince tare da yin afuwa da karbar tubabbun mayakan. Yayin da Zulum ya ce taron ya zama dole ne biyo bayan martanin da suka biyo bayan mika wuyan da mayakan Boko Haram suka yi.
A nashi ra’ayin dangane da matsalar, Dr. Umar Goni, mallami a Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ya ce, abu na farko da ya kamata a sani shi ne: Shin me dalilin da yasa aka sako su, kuma su waye suka sako su cikin jama’a? Saboda idan kaji batun afuwa to an yi ba daidai ba kenan.
Sannan ya kara da cewa: shin me shari’a ta ce dangane da yiwa mai laifi afuwa; wanda yayi kisan ganganci ne za a yiwa afuwa ko wanda yayi kananan laifuka? Ya ce, “Domin akwai alamun cewa babu shugabanci nagari a Nijeriya, saboda da ace akwai da hakan ba zai taba faruwa ba.”
Shehin Mallamin Jami’ar ya kara da cewa, “Amma tunda an riga an sako su cikin jama’a, abin da zamu ce shi ne su san yadda zasu zauna cikin jama’a, suma jama’ar gari suyi hakuri domin abin yafi karfin jama’a, amma ba don haka ba abin zai canza zuwa wani abu daban.”
“Sannan kuma zai yi wuya mu’amalarsu da jama’a ta tafi yadda aka saba a baya, saboda mummunan ta’addancin da suka yi na kashe-kashe. Kuma ina mai nanata maka cewa abin ne yafi karfin mutane babu yadda za su yi tunda gwamnati ta angizo su cikin su karfi da yaji. Amma har yanzu mutane suna dar-dar dasu.”
“Duk da haka, ni kaina ban yarda munyi mu’amala dasu ba, kuma bani da aniyar na hadu dasu, balle wata alaka ta shiga tsakaninmu. Kuma shi yasa na gaya maka cewa wannan tsarin bai yi ba sam; kuma dalilina shi ne, an kawo ne haka kawai ba tare da an zaunar dasu tare da kwararrun masana halayya da goge miyagun dabi’u ba, ko wasu mallaman da zasu yi musu nasiha da tunatarwa mai ratsa zukata ba.”
“Amma zancen da Gwamna Zulum yayi cewa kashi 90 cikin dari ya aminta da tuban tsoffin yan ta’addan siyasa ce kawai, sannan aron bakin talakawa ne ya ci musu albasa. Kuma mun yi masa uziri a matsayin sa na Shugaba.
“Amma abin tambaya a nan shi ne, shi (Zulum) aka yi wa laifi ko mutanen jihar Borno? Idan ya fadi hakan, to su kuma wadanda aka kashe musu iyaye, yan uwa da yaya da makamantan su; wasu an yi musu fyade an yiwa matan wasu, yayan wasu a gabansu; shi ne wani zai fito a rana tsakiya ya ce ya yafe musu- a madadin su wa aka yi wannan yafiyar?”
“Wannan kawai gwamnati ce ke kidanta tana rawarta da kanta; babu ruwan talaka a wannan sabgar. Amma idan ra’ayin jama’a za a bi kamata yayi a ware wadanda suka yi kisa daba daga cikin tubabbun, a ware wadanda aka tilastawa shiga Boko Haram, sannan a ware masu kananan laifuka- sai shari’a tayi aikinta a kansu. Amma ban ga dalilin da zai sa a sako wanda ya aikata laifukan kisa cikin mutane ba.”
A nashi bangaren kuma, Hakimin Jere, Alhaji Ibrhim Waziri ya bayyana wakilinmu cewa, sakamakon addu’ar Allah ya kawo saukin matsalar tsaron da ta addabi jihar Borno, ta taimaka wajen nasarar shawo kan mayakan wajen mika wuya ga gwamnati kuma ta karbi tubansu.
“Kamar yadda gwamnati tayi muna bayani, tubabbun mayakan sun kasu gida-gida; akwai wadanda ake rike dasu a daji suna yin noma ana saya amfanin gona a hannun su, akwai wadanda tilasta musu aka yi karfi da yaji, sannan akwai masu amfani da makamai tare da yakar garuruwa.”
“Saboda haka idan sun mika wuya: ana gudanar da cikakken bincike wajen mambanta tsakanin wadanda suka dauki makami da wadanda tilasta musu aka yi a tsarin yin afuwar. Shi ne sai a kai wadanda suka dauki makamai zuwa Gombe domin a sake saita tunanin su. Su kuma sauran sai a mayar dasu cikin al’umma.”
“A nan karamar hukumar Jere, duk da tubabbun mayakan basu da yawa sosai, amma akwai su kuma suna harkokin su tare da jama’a. Kuma hakan ya zo ne sakamakon irin yadda gwamnati ta bai wa abin karfi wanda talaka bashi da wani zabi face dole ya bi abin a haka.”
“Sannan duk da hakan jama’a suna kaffa-kaffa da mu’amala da tubabbun mayakan, saboda yadda zaka gansu yau amma bayan kwana biyu ko uku sai ka nemesu ka rasa; sun koma (duk da bamu san inda suke komawa ba).”
Hakimin Jere ya bayyana cewa, a matsayin su na shugabanin al’umma, shawarar da ya dace mu bai wa gwamnati shi ne ta kula da mutanen da suka rasa yan uwansu, suka yi asarar dukiyoyinsu da dukan abin da suka mallaka. To idan an tallafa wa mayakan, suma wadanda suka yi wadannan asarar ya kamata a tallafa musu kuma ayi musu wa’azi da nasiha.”
“Sannan idan ba a yi hakan ba; kawai an tallafa wa tubabbun mayakan tare da kai su cibiyoyin basu horo, amma an manta da daya bangaren, daga baya abin ba zai yi kyau ba.”
A yan kwanakin nan, wasu daga cikin tubabbun mayakan Boko Haram, wadanda suka ajiye makaman su; dake zaune a birnin Maiduguri, sun yi barazanar sake komawa inda suka fito matukar gwamnati ta kasa cika musu alkawuran da ta dauka, na basu gidaje da kudaden kama sana’o’in da za su dogara da su.