Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya ce gwamnatinsa ta ware Naira Biliyan 3.5 domin biyan sauran makudan kudade ga ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar.
Gwamna Bagudu ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a dakin taro na masu ruwa da tsaki akan kasafin kudin jihar na shekarar 2023 da aka gudanar a dakin taro na masaukin Shugaban kasa a Birnin Kebbi.
- Bagudu Ya Amince Da Nadin Sarakunan Gargajiya 2 A Masarautar Yauri Ta Jihar Kebbi
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Noma A Matsayin Dan Takarar PDP A Kebbi
A cewar gwamnan, gwamnatin jihar za ta biya wadanda suka yi ritaya basussukan kudaden da suka bi tun daga watan Disambar 2021 har zuwa watan Satumba 2022.
Bagudu, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi kwakwarar shiryi don ganin an biya kudaden kafin karshen wannan shekarar.
Bugu da kari ya ce “Dole ne in gode wa ma’aikatan gwamnati da daukacin al’ummar jihar bisa nuna goyon baya da hadin kai da suke yi.