Jami’an Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), a ranar Juma’a, sun kama wasu mutane 18 da ake zargi da yin damfara a yanar gizo a wani samame da suka kai a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Wadanda aka kama sun hada da Adeleye Ayodeji, Muhammed Ayub, Odelade Samuel, Sodiq Olanrewaju, Ola Francis, Adeniyi Damilare, Olalekan Samad, Tunde Ayodele, Zubair Buhari da Oladosu Naheem.
- Peng Liyuan Ta Ziyarci Dakin Adana Kayan Tarihi Na Fasaha Na Birnin Ayutthaya Na Thailand
- Sin Ta Zama Misali A Fannin Inganta Ci Gaban Kasa Da Kasa
Sauran sun hada da Olowokere Jamiu, Lawal Usman, Jamiu Abdulrasaq, Lawal Ahmed, Opeyemi Samuel, Alarape Ahmed, Kolawole Daniel da Ganiyu Taofeek.
An kamo da wadanda ake zargin ne daga maboyarsu da ke Sobi, Akerebiata da ke rukunin gidaje na Las Vegas yankin Asa Dam na Ilorin.
Wadanda ake zargin, wadanda galibinsu matasa ne, sun hada da dalibai shida na manyan makarantun jihar, dan wasan kwallon kafa, mai zanen kaya, dillalin Bitcoin, mai wanki da dan caca ta yanar gizo, da dai sauransu.
Bayan kama su, an kwato wasu manyan motoci guda biyar, wayoyin hannu daban-daban guda 32 da kwamfuta guda takwas.
EFCC ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken da ake yi.