Sabon kwamishinan zabe na Jihar Kano na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Ambasada Zango Abdu, ya ce INEC ta gama kimtsawa tsaf domin gudanar da sahihi kuma ingataccen zabe a jihar a zaben 2023.
Kan hakan ne kwamishinan, ya ce zuwa yanzu wadanda suka yi rijistar katin zabe kuma suka cancanci kada kuri’a a Jihar Kano sun kai mutum miliyan 5,927,565.
- Lauyoyin Arewa Sun Zargi EFCC Da Nuna Wariya Kan Wadanda Ake Zargi Da Badakalar Kudade
- INEC Ta Roki ‘Yan Jarida Da Su Kauce Wa Labarai Da Dumi-Dumi Da Zafafan Kanun Labarai Don Jawo Hankali
Ambasada Abdu, ya bayyana haka ne a lokacin da ke ganawa da masu ruwa da tsaki a dakin taro na ofishin INEC da ke Kano a ranar Juma’a, inda ya ce sun gama shiri wajen gudanar da ayyukansu bisa yadda kundin tsarin mulkin kasa da dokokin zabe suka tanadar.
Abdu ya yi bayanin cewa, dokar zabe sashe na 19 (1) da (2) na dokar zabe ta 2022 ya tanadar da cewa hukumar zabe za ta wallafa kwafin sunayen wadanda suka yi rijistar zabe a kowacr rumfar rijista da ke gudunma da kananan hukumomi.
Bisa wannan dokar, ya ce hukumar ta samar da kwafi na jerin wadanda suka yi rijistar kuma tuni ta manna su a kowace cibiyar rijista guda 484 da ke cikin gundumomi da suke fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Ya bai wa dukkanin jam’yyun siyasa a jihar tabbacin gudanar da zabe mai cike da gaskiya da adalci.
Ya bukaci masu ruwa da tsakin da su bai wa hukumar hadin kai da goyon baya domin ta samu nasarar cimma wannan manufar ta tabbatar da ingataccen zabe a fadin jihar.
Shi kuma a bangarensa, sabon kwamishinan ‘yansandan Jihar Kano, CP Maman Dauda, ya ce, za su yi aikin hadaka da sauran hukumomin tsaro a jihar don tabbatar zaben ya tafi cikin kwanciyar hankali da tsaro.
Ya yi gargadin cewa duk mai niyyar kawo yamutsi da harigido a lokacin zaben gara ya gaggauta sauya matsayarsa domin ba zai samu gurbin hakan ba.