ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Gano Halittar Da Ta Fi Girma A Duniya

by Idris Aliyu Daudawa
4 years ago
DUniya

Ka bar maganar dabbar ruwan nan da ake kira ‘blue whales’ da Ingilishi da manya-manyan bishiyoyin jan katako. Babbar halitta mai rai da aka sani, ta kai girman fadin sama da mil biyu, kuma da wuya ka tada ganinta.

Kwararran kukun nan (mai dafa abinci) na kasar Italiya Antonio Carluccio ya ce tana da dadi sosai idan aka ci ta da taliya da kuma jan barkono. Amma kuma a wajen masu lambu barazana ce ga furanninsu da sauran abubuwan da suke shukawa.

  • Kwanturola-Janar Na NIS Ya Amince Da Nadin Tony Akuneme A Matsayin Sabon Kakakin Hukumar Na Kasa
  • Adabin Zamanin Da Na Sin (3)

Wannan halitta ta shuka (honey fungus) wadda wani nau’i ne na abin da wasu ke kira naman gwari ko naman kaza (mushroom), ba raba kan masana kawai ta yi ba, ana kuma yi mata kallon halitta mai rai da ta fi girma a doron duniya.

ADVERTISEMENT

A takaice ita wannan shuka da ake kira da harshen Inglishi ‘honey fungus’ a fadi ta kai girman mil 2.4 ko kilomita 3.8 a yankin Blue Mountains na Oregon da ke Amurka.

Nau’uka daban-daban na wannan tsiro (fungi) da aka fi sani da sunan na Ingilishi ‘honey fungus’, suna kashe bishiyoyi da sauran shukoki na katako (manyan bishiyoyi) da yawa.

LABARAI MASU NASABA

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum Kan Zargin Tono Gawa Daga Kabari A Kebbi

Yadda Ɗa Da Uwa Suka Ɗauki Hayar Wani Don Ya Kashe Mahaifinsa A Kano

Tarin tsirran wannan halitta da ake gani a kan kasa (fili), wani sashe ne na ‘ya’yan itace na wannan shuka mai girman gaske da ke karkashin kasa.

Duk tsawon lokaci sai a ‘yan shekarun nan ne masana kimiyya suka gano yadda girman wannan shuka yake.

Mai kashe bishiyoyi:

A shekarar 1998 wani ayarin ma’aikatar kula da gandun daji ta Amurka, ya shiga binciken dalilin da ke sa wasu bishiyoyi masu yawa suke mutuwa a gandun dajin

Malheur da ke gabashin Oregon.

Masu binciken sun gano yankin da abin ya shafa ta hotunan da suka dauka ta jirgin sama, kuma suka tattara samfur na bishiyoyin da suka mutu da kuma wadanda suka kusa mutuwa har 112. Binciken da aka yi ya nuna dukkanin bishiyoyin in banda hudu wannan shuka ce (armillaria solidipes) ta kama su.

Idan wata saiwa ta wannan shuka ta hadu da wata wadda suke da irin kwayoyin halitta iri daya, sai su hade su haifar da shuka daya.

Masanan sun yi amfani da wannan ilimi, wajen sanin wadanne ne suke hadewa kuma wadanne ne ba sa hadewa, daga nan sai suka gano cewa tarin saiwa iri daya masu kwayoyin halitta iri daya ne suka harbi bishiyoyi 61 daga cikinsu (wadanda suka mutu da wadanda suka kusa da mutuwar).

Tsakani mafi girma daga shuka daya zuwa wata shukar ta wannan tsiro ko halitta shi ne mil 2.4 ko kilomita uku 3.8.

Masu binciken sun yi lissafi suka ga wannan shuka (Armillaria solidipes) ta yadu a filin da ya kai fadin murabba’in mil 3.7 ko kilomita 9.6, kuma ta kai tsakanin shekara 1,900 da 8,650.

A wannan lokaci kafin a gano wannan ta yanzu, halittar da aka sani mafi girma a duniyar, ita ma shuka ce wadda suke nau’i daya, wadda aka gano a 1992 a Kudu maso Yammacin Washington, ita kuma ta yadu har zuwa fadin murabba’in sama da kilomita shida da rabi.

Masana ilimin halittu sun dade suna muhawara a kan mizani ko ma’aunin da za a yi amfani da shi wajen ayyana halitta guda daya, wato a ce wannan halitta zaman kanta take yi, ita kadai ce ba ta yi tarayya da wata ba.

A kan haka ne ita wannan shuka, ta cimma wannan matsayi na zama halitta daya mai zaman kanta saboda gaba dayan wannan fili da ta mamaye a karkashin kasa dukkanin saiwowin suna da kwayar halitta iri daya ne, sannan suna iya sadarwa tsakaninsu, wanda hakan ke nuna suna da manufa daya ko kuma akalla suna aiki tare.

Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum Kan Zargin Tono Gawa Daga Kabari A Kebbi
Al'ajabi

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum Kan Zargin Tono Gawa Daga Kabari A Kebbi

November 25, 2026
Yadda Ɗa Da Uwa Suka Ɗauki Hayar Wani Don Ya Kashe Mahaifinsa A Kano
Al'ajabi

Yadda Ɗa Da Uwa Suka Ɗauki Hayar Wani Don Ya Kashe Mahaifinsa A Kano

August 14, 2026
Ana Zargin Jami’in Kwastam Da Kashe Kansa A Bauchi Saboda Damuwa
Al'ajabi

Ana Zargin Jami’in Kwastam Da Kashe Kansa A Bauchi Saboda Damuwa

June 9, 2026
Next Post
Za A Haramta Amfani Da Sinadarin Da Ke Sa Dariya Da Nishadi

Za A Haramta Amfani Da Sinadarin Da Ke Sa Dariya Da Nishadi

LABARAI MASU NASABA

2027: Ba Zan Je Majalisa Don Faɗa Da Gwamnatin Tarayya Ba – Bala Muhammad

2027: Ba Zan Je Majalisa Don Faɗa Da Gwamnatin Tarayya Ba – Bala Muhammad

November 26, 2026
MDD Ta Ce Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Amfani Da Sararin Samaniya Cikin Kwanciyar Hankali

MDD Ta Ce Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Amfani Da Sararin Samaniya Cikin Kwanciyar Hankali

November 26, 2026
Tinubu

Tinubu Ya Bai Wa Iyalan Waɗanda Suka Mutu A Hatsarin Jirgin NAF A Ondo Gidaje Da N100m Ga Kowanne

November 26, 2026
An Fitar Da Jerin Biranen Dake Zaman Cibiyoyin Kirkire-kirkiren Kimiyya Da Fasaha Na Duniya

An Fitar Da Jerin Biranen Dake Zaman Cibiyoyin Kirkire-kirkiren Kimiyya Da Fasaha Na Duniya

November 26, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Tsadar Makamashi Na Ƙara Jawo Tsadar Gidaje — Atiku

November 26, 2026
Kasar Sin Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa A Fannin Binciken Sararin Samaniya

Kasar Sin Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa A Fannin Binciken Sararin Samaniya

November 26, 2026
Ba Za Mu Taɓa Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba, In Ji Gwamnan Zamfara

Ba Za Mu Taɓa Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba, In Ji Gwamnan Zamfara

November 26, 2026
Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Zargi Japan Da Yin Kafar Ungulu Ga Zaman Lafiya Da Daidaito A Yankin Asiya Da Fasifik

Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Zargi Japan Da Yin Kafar Ungulu Ga Zaman Lafiya Da Daidaito A Yankin Asiya Da Fasifik

November 26, 2026
Gwamnatin Nasarawa Ta Yi Rajistar Laifukan Cin Zarafin Mata 888 Cikin Watanni Tara

Gwamnatin Nasarawa Ta Yi Rajistar Laifukan Cin Zarafin Mata 888 Cikin Watanni Tara

November 26, 2026
Sin Na Fatan Ci Gaba Da Koyo Daga Juna Da Karfafa Fahimtar Juna Tsakaninta Da Kasashen Afirka

Sin Na Fatan Ci Gaba Da Koyo Daga Juna Da Karfafa Fahimtar Juna Tsakaninta Da Kasashen Afirka

November 26, 2026

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.