Al’adun daular Tang sun kai matsayin koli na al’adun kasar Sin,musamman ma lokacin samun bunkasuwar wakokin gargajiyazuwa wa’adin samun bunkasuwar daular Tang a duk fannoni.
A cikin tarihin daular Tang na tsawon sama da shekaru 300, ansamu wakoki sama da dubu 48.9 da suka yadu a lokaci mai zuwa.
- Sin Ta Zama Misali A Fannin Inganta Ci Gaban Kasa Da Kasa
- Oramah, Marwa, Amusan Sun Yi Nasarar Zama Gwarazan Kamfanin LEADERSHIP A 2022
A sakamakon haka, an samu fahimtar sunayen marubutawakoki sama da 2300 bisa wadannan wakokin daular Tang.
A fannin samar da wakokin daular Tang, an dora muhimmancikan hakikanin abubuwa da ba na gaskiya ba tare.
A fanninsalolinsu kuma, akwai salo mai jimloli 4 da na jimloli 8, akowace jimla, akwai kalmomi 5 ko kalmomi 7.
Bugu da kari, ansamar da wakokin karni na kusa da yanzu masu dadi sosai.
A cikin marubuta wakokin daular Tang, Li Bai da Du Fu sunfi shahara, kuma sun sami suna a duk duniya.
A kan kira su biyu“Li-Du”.An kira Li Bai Waliyin wakoki, wanda yake da kwarewasosai.
Wakokin da ya rubuta cike suke da abubuwan kaga. Sunnuna alfahari ga ni’imtattun wurare na kasar.
An samu wakokinLi Bai sama da 990 a yanzu. A cikinsu, wakar “Qiangjinjiu”,da wakar “Shudaonan”, da wakar “Duba magangarar ruwa daketsaunin Lushan” da dai sauransu, sun shahara kwarai da gaske.An kira Du Fu Sarkin wakoki.
A yayin da yake wani karaminmatashi, ya kai ziyara wurare daban daban masu ni’ima. Ammadaga bisani, ya gamu da matsaloli da yawa a cikin rayuwarsa.Sai a kai a kai ya samu fahimtar kalubalolin da jama’a su kangamu da su.
A sabili da haka, a cikin wakokinsa, ya kan bayyanawahaloli masu tsanani da jama’a suke sha a cikin zaman rayuwa.An samu wakoki na Du Fu sama da 1400.
A ciki, wakoki mafishahara su ne wakar “Chunwang” da wakar “Tafiyar motocinsojoji”, da wakoki uku dangane da jami’ai (Wakoki uku masusuna “Jami’an Shihao”, da “Jami’an Xin’an”, da “Jami’anTongguan”), da wakoki uku dangane da yin ban kwana (Wakokiuku masu suna “Yin Ban Kwana da iyali”, da “Yin ban kwanabayan aure ba da dadewa ba”, da “Yin ban kwana da tsoho”) dadai makamantansu.Bayan haka, shahararrun marubuta wakoki na daular Tangsun hada da Wang Wei, Bai Juyi, Lihe, Li Shangyin, da Du Mu,da dai sauransu.
Ya zuwa yanzu, wakokin daular Tang sun samu karbuwarjama’a kwarai da gaske.
Har ma wasu daga cikinsu ko yarasuna iya rerawa. Kamar waka mai suna “Yin la’akari a lokacindare”da Li Bai ya rubuta.
A cikin wannan waka, an rubuta yaddaake begyen gari. A cikin wannan waka, an rubuta cewa, an yiruwan sama a lokacin dare na yanayin bazara. Sannan waka maisuna “Yin farin ciki domin ruwan sama a lokacin dare na yanayinbazara” (Wannan jimla ta zo daga waka mai suna “Hawanhusumiyar Guanque” da Wang Zhihuan, marubuci daban yarubuta) da dai sauransu. A kan yi amfani da wasu shahararrunjimloli dake cikin wakokin daular Tang, kamar “Idan ana nemankara hangen nesa, sai a kara hawan hawa daya na husumiya”(Wannan jimla ta fito daga waka mai suna Qiangjinjiu da Li Baiya rubuta), da “Ruwan Rawayan Kogi ya zo daga sararin sama”(Takardar rufin maficici dake bayyana abubuwan dake cikinwakokin daular Tang) da dai sauransu.
Dadin dadawa, littafimai suna Wakokin daular Tang guda 300 ya fi samun karbuwarjama’ar Sin da ta ketare a yanzu.
A kasar Sin a yau, akwai wanikarin magana da cewa, “Idan ana iya karanta wakokin daularTang guda 300, sai ana iya samar da wakoki”.
Ta haka ana iyaganin cewa, Sinawa suna son wakokin daular Tang kwarai dagaske. Ga wasu wakokin daular Tang:Yin la’akari a lokacin dareLi BaiAn yi hasken farin wata a gaban gado,Sai an nuna tababa da cewa ko wannan ne hazo a kasa.An ta da kai domin duba duniyar wata,Sai an kada kai tare da begyen gari.
Wakar Jueju
Du FuTsuntsaye iri na Oriole masu launin rawaya guda biyu sunayin murya a kan wani itacen Willow mai launin kore,Wani ayarin tsuntsayen Egret masu launin fari suna tafiya asararin sama.
Ana iya ganin kankara dake dutsen Min a yamma ta taga, A gaban kofa kuma akwai wani jirgin ruwa da zai tashi zuwakasar Wu ta gabas.
Wakokin daular Song
Wakar Ci, na daya daga cikin salolin wakokin gargajiyarkasar Sin. Akwai sunayenta da dama, shi ya sa ana iya sa matakide-kide domin rera. Shi ya sa a kan kira ta kidan Ci.
Akwaibambanci sosai tsakanin tsawon jimloli. A sakamakon haka, akan kira ta Wakar jimloli masu tsawo da gajere.
Duk wadannansunaye sun bayyana dangantakar kut-kut dake tsakanin wakarCi da kide-kide, da kuma hanyar ta daban da wakar Ci take bi.Bayan haka, Ci na da sunayen sauti da dama, wadanda a kankira su Cipai, kamar “Duniyar wata dake yammacin kogi”,da “Launin ja dake kogi baki daya”, da “Rumengling” da daisauransu.A matsayin waka mai sabon salo, wakar Ci ta kai matsayinkoli a yayin daular Song.
Kamar yadda wakokin daular Tangsuke, wakar Song ita ma tana da muhimmanci kwarai da gaske atarihin adabin kasar Sin.
A lokacin samun ci gaba, an samu marubuta wakar Songmasu nuna fifiko da dama, kamar Su Shi, da Li Qingzhao, daXin Qiji, da Lu You da dai sauransu.
Wakokin Su Shi na da alamar ba kowa masu laushi. Kumasun shafi fannoni iri daban daban, wasu sun bayyana burinsa naba da gudummawa ga kasar, wasu sun bayyana abubuwan dakekauyuka, yayin da wasu kuma suka bayyana ra’ayoyin jama’ana bakin ciki.
Li Qingzhao
Li Qingzhao, shahararriyar marubuciya ce ta daular Song.Wakokinta na da danye, tare da hakikanin tunani.
Wasu sunbayyana fahimtarta ga soyayya da burinta a wannan fanni, wasusun bayyana tasirin da canzawar halittu ta yiwa mutane, yayinda wasu kuma suka bayyana kalubalolin da aka gamu da su asakamakon lalata kasa da iyalai.
Shahararun jimloli da dama sunbayyana kwarewar Li Qingzhao, kamar“Ko ka sani? Kamata yayi a kara samun ganyaye masu launin kore a maimakon furannimasu launin ja”(Wannan jimla ta zo daga wakar Li Qingzhao maisuna “Rumengling”, wadda ta bayyana abubuwan dake yanayinbazara), da “Ba za a iya kawar da damuwata ba.
Da zarar akakawar da ita daga gira, sai ta shiga cikin zuciya” (Wannan jimlata zo daga wakar Li Qingzhao mai suna “Yijianmei”, wadda tabayyana begyenta yadda ya kamata) da dai makamantansu.Xin Qiji, marubucin daular Song da ya fi samun wakokinCi. Mafi yawan wakokinsa, cike suke da jaruntaka.
Jimloli dadama, kamar “Bayan da na sha giya, na fara wasan takobi, saina yi mafarki kamar na dawo rundunar soja” (Wannan jimla tazo daga wakar Xin Qiji mai suna “Pozhenzi”, wadda ta bayyanajaruntakar yaki da sojojin kasar Jin da samun sakamakon maikyau da bautawar kasar, tare da bayyana ma’anar fushi dominrashin damar cimma burinsa), da “Babban tsauni mai launin koreba su iya hana tafiyar ruwa ba, wanda ya nufi gabas a karshe.”(Wannan jimla ta zo daga wakar Xin Qiji mai suna “Pusaman”,inda aka waiwaye babbar matsalar da hare-haren da sojojinkasar Jin suka yi suka samar ga jama’ar kasar, tare da bayyanabakin cikinsa na rashin samun damar shiga rundunar soja dominyaki da sojojin kasar Jin) da dai sauransu, ba ma kawai sunbayyana rayuwar sojoji ba, har ma sun bayyana burinsa na yaki da kasar Jin da tunaninsa na son kasa.
Wakokinsa da dama sun kara abubuwa da tunani da salolin fasaha da yawa na wakokinCi na daular Song.
Kawo yanzu dai, wakokin Song Ci na samun karbuwarjama’a kwarai da gaske. Kusan a kowane iyali, ana iya samunlittafin “Wakokin Song Ci guda 300”.
Dadin dadawa, an tsarasabbin kide-kide ga wasu daga cikinsu domin rera.
Sautin Shuidiao Getou
Yaushe za a iya samun farin wata mai haske? Na tambayi sararin sama tare da giyaa hannu.
Ba a san lokacinfadar dake sararin samaa yanzu ba. Ina son in tafizuwa fadar bisa iska. Ammaina jin tsoro da cewa, gineginendake sararin sama nada sanyi sosai.
Na yi rawarjiki, kasancewa a yankinbil’adam ya fi komawafadar dake duniyar wata.Duniyar wata tana tafiyaa ko ina ba tare da yin barciba.
An yi hasken duniyarwata a gaban taga, tare damutumin dake gado, wandaba zai iya shiga barci ba.
Bai kamata farin wata maihaske ta nuna damuwasosai ba. Amma ina dalilinda ya sa ba ta yi siffar da’iraba sai lokacin da aka yiban kwana.
Mutane su kansamu canzawar rayuwa,kamar yin bakin ciki, dayin farin ciki, da yin bankwana, da yin haduwa,yayin da duniyar wata takan yi canzawar siffarta.
Ba za a samu sauyawa kanwadannan al’amura ba. Inafatan kowa zai samu alheri,tare da duba farin watamai haske sosai, ko akwainisanta a tsakaninsu.