Wani fitaccen jigo a jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, Sanata Magnus Ngei Abe, ya bayyana cewa, jam’iyyar a matakin jihar za ta dukufa wajen nemo kuri’u miliyan daya don goyon bayan dan takarar shugaban kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu a babban zaben 2023.
Abe ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi sa’ilin da yake ganawa da daruruwan mambobin APC da magoya bayan jam’iyyar a filin Jirgin kasa da ke Fatakwal bayan dawowarsa daga Abuja.
Abe dai ya taka rawa sosai wajen gangamin yakin neman zaben tikitin Shugaban Kasa na jam’iyyar ga Tinubu har zuwa lokacin samun nasararsa a lokacin zaben fitar da gwani da ya gudana a Abuja.
Ya jawo hankalin al’ummar jihar da su yi rijistan mara baya wa shirin ‘Project SMA 2023’, mai manufar bai wa jama’a damar zabin wanda zai zame musu gwamna a 2023.
Abe ke cewa: “Kai tsaye zan wuce kauyena domin yin rijistan goyon bayan Sanata Magnus Ngei Abe. Za mu yi rijista wa mutum miliyan daya da za su jefa kuri’a ga Asiwaju Ahmed Bola Tinubu da kuma ni Senator Magnus Ngei Abe.”
Har-ila-yau, Sanata Abe ya yi amfani da wannan damar wajen mika ta’aziyyar sa ga uwar jam’iyyar APC reshen jihar bisa rashin mambobi guda biyu da ta yi masu suna Onimiteim Vincent Samuel da Barrister Prince Loveday Motats.
Abe, a sanarwar da kakakinsa, Parry Saroh Benson, ya fitar, ya misalta mutuwar mambobin jam’iyyar a matsayin babban rashi mai radadi, ya nemi iyalan mamatan da su dauki dangana.