Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta umarci jami’an hukumar da su kama masu karya dokar hana tsala gudun wuce sa’a a kan tituna.
Mai rikon kwarya na rundunar, Dauda Biu, ya bada umarnin a ranar Talata.
- Kamfanin Sinopec Na Sin Ya Kulla Yarjejeniyar Shekaru 27 Da Qatarenergy
- An Bude Dandalin Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Afirka A Birnin Jinhua Na Kasar Sin
Wata sanarwa da jami’in kula da ilimin jama’a na hukumar, Bisi Kazeem ya fitar, ta ce za a kama motocin da suka gaza bin dokar.
Biu ya bayar da umarnin ne biyo bayan wani mummunan hatsarin da ya faru a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu; wanda mutane 37 suka rasa rayukansu.
Kimanin mutane 45 ne a cikin wasu motoci kirar bas Toyota guda biyu da wata motar kirar Golf Volkswagen suka kone.
Sun kunshi maza manya 26, mata 13, yara maza uku da kuma yara mata uku.
“Ragowar wadanda aka ceto su takwas an ceto su da ransu sun samu raunuka daban-daban,” in ji Kazeem.
Hukumar ta bayyana cewa binciken farko da ta gudanar ya alakanta hatsarin da wuce gona da iri da kuma fashewar taya.