Hukumomi a Kasar Indonesiya sun ce adadin wadanda suka mutu ya haura 268, mafi yawa daga cikinsu kananan yara, yayin da har yanzu ba ga mutum 151 ba, yayin da sama da mutum 1,000 suka jikkata.
Masu aikin ceto a kasar na ci gaba da aikin ceto wadanda suka makale a karkashin gini sakamakon girgizar kasa mai karfin gaske da ta auku.
- Kamfanin Sinopec Na Sin Ya Kulla Yarjejeniyar Shekaru 27 Da Qatarenergy
- Yadda Kasashe Masu Ci Gaba Za Su Cika Alkawuransu Yana Da Muhimmanci Wajen Kare Muhallin Duniyarmu
Lalacewar hanyoyi sakamakon girgizar kasar ya sa aikin ceton na tafiyar hawainiya.
Aprizal Mulyadi na makaranta lokacin da iftila’in ya shafi makarantarsu, kuma ya makale cikin ginin makarantar tasu wadda ta rufta sakamakon girgizar kasar.
Dalibin mai shekara 14 ya ce gini ya danne masa mafafunsa to amma bisa taimakon abokinsa ya samu nasarar tsira.
To sai dai abokin nasa ya mutu bayan da shi ma ginin ya danne shi daga baya.
Hukumar kiyaye aukuwar bala’i ta kasar ta ce akalla gidaje 22,000 ne suka lalace, yayin da kusan mutum 68,000 suka rasa muhallansu.
Tuni kasashen duniya; ciki har da Nijeriya suka aike da sakon jajensu ga Indonesia.