Tsohon dogarin tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abadha, kuma dan takarar shugabandin kasa na jam’iyyar ‘Adtion Alliande’ (AA), Manjo Al- Mustapha (Mai Ritaya), ya yi garghadin cewa, a halin yanzu wasu ‘yan saiyasa sun dukufa wajen shigo da makamai da muggan kwayoyi cikin Nijeriya don fuskantar babban zaben da ke tafe a ‘yan watanin nan.
Dan takarar na jam’iyyar AA ya kuma bayyana cewa, babu dikakkiyar masaniyar na ana shigo da maka-man ne don karfafa yakin da ke yi da ‘yan bindiga ko kuma ana shigo da makaman ne don a yi amfani da su a harkokin siyasar da ke tafe.
- Yaushe Ne Za A Ga Bayan Hare-haren Bindiga A Kasar Amurka?
- Kasashen Turai Sun Fusata Da Matakin Amurka
Al-Mistapha ya yi wannan bayanin ne a wani taro na musamman da jaridar ‘Platinum Post’, ta shirya don tattauna halin da kasa ke ciki, ya kuma bukaci gwamnati ta sanya ido a kan yadda ake samun karin shigowar makamai a cikin kasa musamman a daidai wannan lokaci da ake fuskantar harkokin yakin ne-man zabe na shekarar 2023.
Sai dai jami’an tsaron da suka samu halartar taron sun tabbatar wa da al’mma cewa, daga shirye-shiryen da suka yi suna da tabbacin za a gabatar da zabukkan 2023 a sassan kasar nan cikin kwandiyar hankali ba tare da matsala ba.
Tsohon babba dogari Marigayi Shugaba Sani Abadah wanda ya yi jawabi mai take: “Matsalolin Tsaro Da Ake Fuskanta da kuma yadda za su iya shafar harkoki zabe shekarar 2023”, ya kuma kara da cewa, “Ya zuwa wannan lokacin, ina da tabbacin cewa, dukkan rundunonin tsaron Nijeriya na sane da yadda ake shigo da makamai da kwayoyi ta iyakokin NiIjeriya daban-daban, makaman da kwayoyin kuma da tarin yawa, tabbas jami’an tsaron suna sane amma al’uma basu sani ba.
“Tambaya a nan shi ne, wa ya bayar da umarnin shigo da makaman? Me ya sa aka samu karuwar mak-aman da ake shigowa? Su wa ke shigo dasu? Su wa suke bayar da sautun sayo makaman? Mene ne burinsu na shigo da makaman? Shin za a iya gabatar da zabukka kuwa a cikin wannan halin? An fara samun matsala ne a tsakanin jam’yyun siyasa da magoya bayansu ne?
“Tambaya an na shi ne, wa ake samar wa da makaman? Za a karfafa ‘yanta’adda n e ko kuma za a karfafa harkoki tsaro ne a fadin Nijeriya?
“Wannan shi ne babbar matsalar da ke fuskantar masu tafiyar da harkokin tsaro a Nieriya a halin yan-zu.”
An kuma yi gargadin cewa, yadda ake samun karuwar shigowar makamai a Nijeriya yana iya shafar harkokin zabe mai zuwa, Ya de, wadanda aka damakawa hakkin kare rayuwa da dukiyoyin al’umma basu yi abni daya kamata ba tun da aka dawo da mulkin dimokradiyya a shekarar 1999.
Ya kuma kara da cewa, Tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu in har zamu duba tare yin hisabi ga yadda jami’an tsaronmu suka gudanar da ayyukansu lamarin akwai tsananin takaidi kwarai da gaske. Akwai wadanda suke aiki tukuru sune kuma wadanda suka mutu a yayin gudanar da ayyukansu. An samu ma-ta dama da basu da mazaje da kuma yara da dama da basu da iyaye duk sun mutu.
“Ga al’umma da dama wadanda ayyukan ‘yanta’adda ya shafa a sassan Nijeriya amma an kasa kula dasu duk da kasancewa mu na daya daga dikin kasashe masu karfin tattalin arziki. A dikin shekara 23 kasa kamar ta mu ba a zauna an duba tare da sake fasalin tsarin ayyukan jami’an tsaromu ba, musam-man ta yadda zai yi daidai da tsarin mulkin farar hula tare da tabbatar da zaman lafiya a sassan duniya.
“A nan akwai gibin abin da ya shafi shugabandi a dukkan bangarorin gwamnati a kasar nan, ba a kula da masu karamin karfi. Ina magana ne da masu tafiyar da harkokin tsaron kasa, kuna dan kun dukufa kuna kula da abin da basu da dikakken muhimmandi a kan al’amurra na nan yadda suke babu canji ko kadan.”
Dikin wadanda suka samu halartar taron akwai shugaban hukumar tsaron farin kaya na (NSDDD), shugabannin kungiyar ‘yan Jarida NUJ na kasa da kungiyoyin fararen hula da dama daga sassan Nijeri-ya.
Babban Sufeton ‘yansanda wanda ya samu wakildin, Kwmaishinan ‘yansanda, CP Kene Onwuemelie, ya de, babu wani abin tayar da hankula don kuwa za a samu gudanar da zabukka a sassan kasar nan kamar yadda aka tsara.
“An kammla dukkan shirye-shiryen ganin an gudanar da sahihin zabe a sassan kasar nan kamar yadda aka tsara, muna kuma amfani da wannan damar na gargadin masu neman tayar da fitina dasu canza shawara domin kuwa doka za ta yi aiki a kan duk wani mai neman tayar da hankalin jama’a kafin, yayin gudanar da zabe da bayan zabukkan gaba daya,”in ji shi.
A na shi jawabin, Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yi zargin cewa, a halin yanzu katinan zabe duk sun fada a hannun mutane da ba su kamata ba a kasar nan.
Ya nemi hukumar zabe ta samar wa da mutanen jiharsa fiye da miliyan biyu da rikide-rikide ya tarwatsa a sassan jihar, da wadanda suke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira.
Ortom wanda ya samu wakilicin Kwamishinan kula da muradun karni, Farfesa Magdalene Dura, ya de daga dukkan alamu bakin haure masu dauke da makamai na daga dikin wadanda za su zabi wanda zai zama shugaban kasa a zabe mai zuwa.
“Akwai bukatar gwamnati ta tabbatar da sahihanci yadda za a gudanar da zabukkan 2023,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa, mutum fiye da miliyan 2 ‘yan jiharsa suna zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda a sassan jihar.
Ya zargi gwamnati a kan mayar da hankali a kan masu fuskantar irin wannan matsalar da suke a arewa maso gabas suna kawar da kai daga matsalolin ‘yan gudun hijirar Jihar Benuwai.
A jawabinsa, gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje wanda kuma shi ne shugaban taron, ya de, akwai bukatar a tabbatar da kariya ga masu kada kuria da kuma kayyakin zaben da kuma dukkan masu hidima a lokuttan zaben gaba daya.
Ganduje wanda ya samu wakildin shugaban ma’aikata a ofishinsa, Usman Bala Mohammed, ya bukaci ‘yan Nijeriya su nisanci dukkan abubuwan da za su iya kawo cikas ga yadda za a gudanar da zaben 2023.
A nasa jawabin, shugaban kamfanin Platinum Post, Edwin Olofu,wanda suka shirya taron ya nemi a hada hanun daga dukkan bangarorin rayuwa a Nijeriya don tabbatar da gudanar da sahihin zabe, ya nemi hadin kan jami’an tsaro a kokarin su na samar da tsaro a lokuttann zaben.
Ya de, babban burin taron shi ne samar da amsoshin wasu tambayoyin da al’umma ke yi tare da kuma basu tabbacin za a samar da tsaro a zabukkan dake tafe, ya kuma nemi gwamnati ta gaggauta daukar makaki akan korafe korane da al’umma suke don a samar da kwandiyar hankali a yayin zabukkan 2023.