• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda ‘Hackers’ Ke Amfani Da Smishing Wajen Yin Kutse

byIbrahim Sabo
3 years ago
Kutse

A kullum madatsa ‘Hackers’ suna bin hanyoyi daban-daban wajen ganin sun yi kutse a mutane. Kutsen kuwa ya hada da shafukan sada zumunta kuma har da asusun ajiya na Banki.

Wata hikimar da suke yi wajen yin datsa (Hacking) wadda ta yi kaurin suna a wannan lokacin da ake kira smishing ta sanya mutane da dama a halin ha’ula’i, duba da yadda ake yaudararsu don cutar da su.

  • Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Takwaransa Na Kasar Cuba
  • ‘Yansandan Sun sun Cafke Wasu Jami’an EFCC Na Bogi A Delta

Smishing wata dabarar kutse ce da ‘yan madatsa, wadanda aka fi sani da hackers su ke amfani da ita wajen yaudarar mutane. Suna amfani da wannan dabarar ne wajen yaudarar mutane ta hanyar tura musu sakonni ana tambayarsu game da wadansu bayanansu na sirri.

Irin wannan kutsen yana daga cikin ire-iren kutsen Social Engineering da ya addabi mutane. Don haka mutane da dama suna yawan korafe-korafe a kan yadda ake musu kutse ta hanyar shiga asusansu ba tare da saninsu ba.

Sai dai duk da haka, abin da ba a sani ba shi ne, mutanen ne da kansu ke bayar da bayanansu da hanunsu.

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Hanya mafi sauki da madatsan kan bi wajen rudar mutane ita ce tura musu sakonni, musamman zuwa asusun sakonninsu (inbod) na waya da ke nuna kamar sakon yana da inganci, misali; sako daga 500, ko 424 ko makamancin haka. Wato dai wani code, wanda ke nuna cewa ba daga lambar waya bane, don kar a gane su.

Irin wadannan sakonnin suna tunzura mutum ya bayar da bayanansa na sirri, musamman idan aka dubi lambobin da aka yi amfani da su wajen tura sakonnin. Ta wannan hanyar mutum zai yi tunanin daga wani kamfani ne ake neman bayanansa.

Akwai wasu kalmomi da suke kamanceceniya da smishing, wadanda duk suka kasance ire-iren dabarar kutse Social Engineering kamar haka:

  1. Smishing — Tura sakonni zuwa asusun sakonnin waya don rudar da mutane tura bayanansu na sirri zuwa ga madațsa.
  2. Phishing — Tura wa mutane likau, manhajoji ko sakonnin email don karbar wasu muhimman bayanansu na sirri.
  3. Bishing — kiran mutane a waya ta hanyar bi da lallami da kalaman yaudara don damfararsu, musamman don samu bayanansu na sirri.

Ta Yaya Mutum Zai Kare Kansa?

  1. Kada a danna likau ko shafin yanar gizon da ba a yarda da su ba.
  2. Kada a mayar da martani ga sakon imel din da ba a yarda da shi kuma ba a san wanda ya turo shi ba.
  3. Kada a kula da kiraye-kirayen wayoyin da ba a san su ba.
  4. A rinka kula da shafukan da ake ziyarta da tabbatar da sahihancinsu.
  5. Kada a sanya manhajar da ba a tabbatar da sahihancinta cikin na’ura ba.
  6. A kula da sakonni a cikin waya kuma kada a mayar da martani gare su.

Tabbas ya zama wajibi a kula da wadannan shawarwari don kada a yi nadama nan gaba, domin yanzu kutse ya zama ruwan dare a wannan zamanin.

Bugu da kari, a rinka kula da sakonnin da ake samu daga banki hakika ba kowane sako ba ne daga asusun banki, sau tari ana iya amfani da wasu dabaru don kutse cikin na’urori don tura wa mutane sakonnin bogi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Next Post
Abubuwan Da Ake Sa Ran Kwamitin Binciken Kananan Asibitoci Zai Gano

Abubuwan Da Ake Sa Ran Kwamitin Binciken Kananan Asibitoci Zai Gano

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version