• English
  • Business News
Wednesday, July 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Ake Sa Ran Kwamitin Binciken Kananan Asibitoci Zai Gano

by Idris Aliyu Daudawa
3 years ago
in Rahotonni
0
Abubuwan Da Ake Sa Ran Kwamitin Binciken Kananan Asibitoci Zai Gano
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar bunkasa kiwon lafiya matakin farko ta kasa ta kaddamar ta kwamiti mai zaman kansa, da zai gano matsalolin da suke damuwar asibitoci a fadin Nijeriya.

Babban jami’i kuma shugaban hukumar NPHCDA, Dakta Faisal Shuaib shi ne ya kaddamar da kwamitin a Abuja Babban Birnin Tarayya, ya bayyana cewa gwamnatocin tarayya, Jihohi, da kananan hukumomi sun sa kudade masu yawa a tsarin tafiyar da kula da lafiyar al’umma matakin farko.

  • Nnamdi Kanu Ya Maka Gwamnatin Tarayya A Kotun Koli 
  • Tinubu Ya Bukaci Manyan Masu Kalubalantarsa Atiku Da Obi Da Su Janye Daga Takara

Sai dai kuma duk da kudaden da suka sa har yanzu basu ga wani cigaban azo a gani ba, tunda har yanzu ana samun mutuwar mata masu juna biyu da kananan yara.

Yace “A shekaru biyu da suka gabata an samu cigaba mai gamsarwa, amma shi ma din bai kai ace an yaba ba, bai kuma dace da abinda ya dace mu samu a matsayinmu na kasa.Wannan shi yasa mu yin aiki tare da gidauniyar Dangote da ta Bill da Gate ga kuma ta Gwamnonin.Ga asusun kula da al’amuran gaggawa na kananan yara na majalisar dinkin duniya, Hukumar lafiya ta duniya,Taraiyar Turai, Bankin duniya,ga kungiyar cigaban kasa da kasa ta kasar Amurka.Hakan shi yasa muke ganin zuwa yanzun muna iya yin magana kan cigaban da aka samu, kan wani alkawarin da aka dauka na Seattle domin mun ga irin gudunmawar da Jihohi suka bada dangane da su kananan Asibitoci”.

Faisal yace wannan shi ne dalilin da yasa suka kasance cikin murna da jin dadi a Hukumar ta kula da lafiya matakin farko ta kasa, ma’aikatar lafiya ta Tarayya da sauran ‘yan kwamitin kulawa suna da mashahuran ‘yan Nijeriya daga Malaman manyan makarantu kan taimakon da suke yi ma al’umma.Ya kara jaddada cewa hukumar tana jiran tayi aiki da kwamitin domin kara bunkasa ayyukan wuraren kula da lafiyar al’umma matakin farko.

Labarai Masu Nasaba

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

Da take jawabi lokacin kaddamarwa jami’a, mai wakiltar ofishin asusun kula da al’amuran gaggawa na kananan yara na majalisar dinkin duniya na Nijeriya, Cristian Munduate ta nuna jin dadinta a kasance cikin wadanda za ayi abinda zai zama tarihi, na kokarin da ake na kara inganta kulawa da lafiyar al’umma,a karkashin Kudurin da aka cimmawa  a zaman taron na Seatle.

Ta ce taron ya cimma dukkan sharuddan da suka kamata shi yasa ma kwamitin da zai lura da bada shawara kai tsaye da yin bayani kan kokarin da kowacce Jiha tayi, domin tabbatar da shi tsarin da aka yi kudurin amfani da shi, ya kasance akwai adalci, rikon amana, da kasancewa ko wanne lokaci aka bukaci sanin halin da ake ciki babu wani bata lokaci za a sani.

“Ta kara jan hankali wajen bayyana yadda hukuma UNICEF ta jajirce da ganin sai an aiwatar da duk matakan da aka dauka lokacin da aka yi taro a Legas dangane da matsalolin da ake fuskanta.Yana da kyau a tuna dacewa dukkan gwamnonin Jihohi 36 sun samu halartar taron da kansu, domin nuna a shirye suke su bada duk gudun mawar da ake son su bada don a cimma burin abinda aka sa gaba”.

Bugu da kari tace UNICEF a shirye take ta hada kai da Nijeriya da duk sauran wadanda ake tafiya tare domin tabbatarwa ‘yan Nijeriya suna samun dukkan abubuwan da suke bukata, na kula da lafiyarsu kamar yadda ya kamata, ba tare da shan wahalar yadda za a samu abin yin amfani wajen neman kula da lafiyar.

Shi ma Babban darekta na kungiyar gwamnoni ta Nijeriya Mista Asishana Okauru cewa yayi kungiyar  bata siyasa  bace, amma tana yin taro aklai- akai domin tattauna al’amuran da   tsare- tsaren da suka shafi abubuwan  kawo cigaban al’umma.

Yace shi kwamitin mai zaman kan da aka kaddamar zai iya gano Jihohi da gwamnonin wadanda suka kasa cimma abubuwan da aka amince da ayi hakan, ya gode masu mabobin kwamitin mai zaman kansa wajen amincewar da suka yi na aiki tare da kungiyar gwamnaoni ta Nijeriya.

“Hakanan ma  a shekarar 2016 Shugabannin kungiyar an karbi bakuncinsu a Ciato wanda gidauniyarby the Bill-gate da Dangote ,wanda daga karshe aka samu  wata matsaya da ake kira da suna  yarjewar Ciato. Babban abinda suka sa gaba shi ne hanyar da za ayi amfani da ita domin tabbatar da duk kudurorin an samu cim masu kamar dai yadda ya bayyana”.

Akauru yace akwai wata tawaga ta wasu kwararru mai zaman kanta wadda zata rika taimakawa wajen tabbatar da duk abubuwan da aka amince za ayi ana aiwatar dasu, sai dai manufa ita ce ana son su yi aikinsu na kwararru ba su sa kansu cikin siyasa ba, shi yasa ma suka hada kungiyoyin biyu domin aiki tare.

A nata jawabin shugabar kungiyar mai zaman kanta da zata rika sa ido kan yadda ake aiwatar da tsare- tsaren Farfesa Florence Ejembi cewa tayi babbar rana ce,domin tun lokacin Ministan lafiya Farfesa Ransom Kuti tun, a shekarar 1986,inda aka fara daukar matakai na kawo gyara a harkar kula da lafiya, wani  mataki nha kula da lafiyar al’umma bai daya bangaren mataki na farko.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BincikeKwamitiSa Rai
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda ‘Hackers’ Ke Amfani Da Smishing Wajen Yin Kutse

Next Post

Ra’ayoyinku A Kan Batun Hako Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe

Related

jam'iyyu
Rahotonni

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

3 weeks ago
Ran
Rahotonni

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

3 weeks ago
Tsadar Rayuwa: Yadda Al’umma Suka Yi Sallah Cikin Kunci
Rahotonni

Tsadar Rayuwa: Yadda Al’umma Suka Yi Sallah Cikin Kunci

4 weeks ago
Ana Fargabar Boko Haram Ta Kara Mamaye Wasu Kananan Hukumomi A Borno
Rahotonni

Ana Fargabar Boko Haram Ta Kara Mamaye Wasu Kananan Hukumomi A Borno

1 month ago
Kokarin Minista Tuggar Na Mayar Da Hijirar Masana Daga Nijeriya Zuwa Kasashen Waje Alhairi
Rahotonni

Kokarin Minista Tuggar Na Mayar Da Hijirar Masana Daga Nijeriya Zuwa Kasashen Waje Alhairi

1 month ago
Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar
Rahotonni

Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar

1 month ago
Next Post
Ra’ayoyinku A Kan Batun Hako Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe

Ra’ayoyinku A Kan Batun Hako Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe

LABARAI MASU NASABA

An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa

An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya

Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya

July 1, 2025
An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin

An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin

July 1, 2025
Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

July 1, 2025
Kayan Aro Baya Rufe Katara

Kayan Aro Baya Rufe Katara

July 1, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100

Askarawan Zamfara Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Bindiga, Kacalla Ɗanbokolo Ubangidan Turji

July 1, 2025
Tawagar Likitoci Ta Sin Ta Ba Da Horon Fasahar Likitancin Gargajiya Ta Sin A Nijar

Tawagar Likitoci Ta Sin Ta Ba Da Horon Fasahar Likitancin Gargajiya Ta Sin A Nijar

July 1, 2025
Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano

Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano

July 1, 2025
Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta 

Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta 

July 1, 2025
An Yi Bikin Kade-Kade Don Taya Murnar Cika Shekaru 104 Da Kafuwar JKS

An Yi Bikin Kade-Kade Don Taya Murnar Cika Shekaru 104 Da Kafuwar JKS

July 1, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.