Yau Lahadi 27 ga wata, tawagar harba kumbon Shenzhou-15, ta shirya wani atisayen hadin gwiwa a daukacin yankin. Kawo yanzu, an kammala ayyukan bincike kan dukkan tsare-tsaren harbawa, da kuma shirye-shirye daban-daban masu nasaba da aiki.
‘Yan saman jannatin kumbon na Shenzhou-14, sun shirya tsaf don maraba da isar takwarorin su na kumbon na Shenzhou-15. Wannan shi ne karon farko da ‘yan sama jannatin kasar Sin za su yi maraba, da kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati a tashar sararin samaniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)