• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin: Ya Kamata Burtaniya Ta Mutunta Gaskiya Kuma Ta Daina Nuna Rashin Adalci

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Dangane da zargin da firaministan kasar Burtaniya Rishi Sunak ya yi kan manufar kasar Sin, game da riga kafin yaduwar annobar COVID-19, ciki har da duka da kame wani wakilin BBC, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Talata 29 ga wata cewa, irin kalaman na Burtaniya sun sabawa gaskiyar lamarin, tare da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, kuma Sin tana adawa da hakan.

Kakakin ya bayyana cewa, ainihin lamarin shi ne, a daren ranar 27 ga wata, domin kiyaye zaman lafiyar al’umma, ‘yan sandan birnin Shanghai sun lallashi mutanen da suka taru a wata mararrabar hanya, da su bar wurin kamar yadda doka ta tanada, ciki har da ‘dan jaridar BBC dake Shanghai.

  • Shugaban Kasar Sin Ya Sha Alwashin Karfafa Hadin Gwiwar Kasarsa Da Rasha A Fannin Makamashi

Ko da yake ‘yan sandan sun bayyana wa ‘dan jaridar karara cewa, suna shirin lallashin mutanen da ke wurin domin su tafi, amma ‘dan jaridar ya ki barin wurin, kuma bai bayyana wa ‘yan sanda matsayinsa na ‘dan jaridar ba.

Don haka, ‘yan sandan suka tafi da shi ala tilas, kana daga bisani suka umurce shi da ya tafi bayan gudanar da tantancewar da ta dace da sanar da shi doka, kuma an aiwatar da hakan ne bisa tsarin dokoki da ka’idoji.

Kakakin ya jaddada cewa, ‘yan jarida na kasashen waje suna da hakkin ruwaito rahotanni bisa doka a kasar Sin, kuma dole ne su bi dokokin kasar Sin, kana ya kamata su nuna katin aikin jarida kafin su bayar da rahoto, kuma bai kamata su aiwatar da wasu ayyukan da ba su dace da matsayinsu ba, kuma hakan ya shafi duk wata kafa ta watsa labarai, kana hakan bai saba da abin da ake kira da ‘yancin aikin jarida ba.

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

Kakakin ya kara bayyana cewa, akwai kafafen yada labarai na kasashen waje da yawa a kasar Sin, abun tambaya shi ne me ya sa har kullum BBC ke samun matsala? Wannan batu ne da ya kamata a yi la’akari da shi sosai. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
Next Post
An Harba kuKmbon Shenzhou-15 Dauke Da ‘Yan Sama Jannati 3

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.