Uwargidan shugaban Nijeriya, Aisha Buhari, ta bayyana aniyarta ta sulhunta bangarorin da ke cikin rudani na jam’iyyar APC a jihar Adamawa.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, rikicin ya barke a jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa tun a watan Mayun da ya gabata bayan zaben fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar da Sanata A’ishatu Dahiru Binani ta lashe, wanda daya daga cikin ‘yan takarar Malam Nuhu Ribadu ya ki amincewa da sakamakon sannan ya garzaya kotu.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Yola a watan da ya gabata ta soke zaben fidda gwanin tare da bayyana cewa jam’iyyar ba ta da dan takarar gwamna a jihar a zaben 2023, lamarin da ya sa jam’iyyar APC da Binani da Ribadu suka garzaya kotun daukaka kara domin daukaka kara kan hukuncin.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Yola, babban birnin jihar Adamawa, a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, ta bayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin halastacciyar ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Adamawa, lamarin da ya kara jefa jam’iyyar cikin rudani a jihar.