Kafar yada labaran kimiyya ta kasar Amurka da ake kira Protocol, ta wallafa wani rahoton da babbar ’yar jarida Kate Kaye ta bayar, bisa binciken da ta gudanar a kwanan baya, inda ta tona yadda Eric Schmidt, tsohon babban jami’in kamfanin Google, ya ci kazamar riba ta hanyar yayata ra’ayin nan na wai “kasar Sin na haifar da babbar barazana ga Amurka ta fannin fasaha.”
An ce, a yayin da yake kan kujerar shugabancin kwamitin tsaron kasar Amurka ta fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, ya yi ta bayyana wa gwamnatin kasar damuwar yadda Amurka din ta gaza a takararta da kasar Sin, ta fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, don sa kaimi ga gwamnati ta zuba makudan kudade a fannin nazarin fasahar.
A sa’i daya kuma, kasancewarsa babban mai zuba jari ta fannin nazarin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, Eric Schmidt ya ci riba mai tsoka bisa ga yadda yake zuba jari a kamfanonin da suka samu kwangila mai tarin kudi daga gwamnatin kasar.
A hakika, Amurka ta dade tana fakewa da batun “tsaron kasa” wajen dakile kamfanin kimiyya na kasar Sin, inda ta mayar da harkokin kimiyya da cinikayya a siyasance kuma a matsayin makami. Kuma faduwar ta zo daidai da zama yadda mutane irin Schmidt suka rika baiwa gwamnati shawarwari na wai “kasar Sin barazana ce”, duk da cewa, ko da gaske ne suna damuwa da tsaron kasarsu, amma dai mun san cewa suna cin kudin yin hakan.
A yayin da mutane irinsu Schmidt suke ta hada kai da ’yan siyasar Amurka, Amurka kuma take kara yin babakere a fannin kimiyya.
Yadda Amurka ke rika siyasantar da harkokin kimiyya da cinikayya, ya keta dokokin cinikayyar duniya, haka kuma ya lalata tsarin samar da kayayyaki, da ma ci gaban harkokin kimiyya a duniya.
A yayin da sassan kasa da kasa ke kara dunkulewa da juna, ya zama dole su hada gwiwa da juna don tabbatar da ci gabansu. Wadanda ke neman toshe hanyoyin wasu, hanyoyinsu ne za su toshe. (Mai zane: Mustapha Bulama)