Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da rabon kudin raya kasa ta biliyan N500 a shiyyoyi shida na bankin raya kasa (DBN) ya yi barazanar bada umarnin kama gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele da wasu shugabannin hukumomin da rabon kudin ya shafa bisa gaza bayyana a gaban Kwamitin.
Bayan gwamnan CBN, kwamitin wanda ke karkashin jagorancin Sani Musa, Sanata da ke wakiltar mazabar (Neja ta Gabas kuma mambar jam’iyyar APC), ya kuma yi barazanar cafke manajan gudanarwa na bankin raya masana’antu (BoI), Olukayode Pitan; manajan darakta na (NIRSAL), Aliyu Abdulhameed da Daraktan-janar hukumar bunkasa kanana da matsaikaitan sana’o’in (SMEDAN) Olawale Fasanya.
Shugabannin hukumomi biyar din an tsammaci bayyanarsu a gaban Kwamitin binciken a ranar Laraba, domin yin bayani kan zargin rashin daidai a rabon kudaden raya kasa ta biliyan N500.
A cewar Musa, hukumomi takwas daga cikin wadanda ake da bukatar bincika kan kudin, an gayyaci biyar daga cikinsu a zaman da kwamitin ya gudanar a ranar Laraba.
“Daga cikin biyar din nan, biyu ne kawai suka zo sauran ukun da CBN, BOI da NIRSAL, ba su zo ba kuma babu wata wasika da suka aiko da ke bayani kan dalilin rashin zuwan nasu.
“Aikin da ke gaban kwamitin nan na da muhimmanci, don haka muna bukatar hadin kai da biyayya ga dukkanin wadanda lamarin ya shafa.”
Ya ce, ministan kudi da kasafi, Zainab Ahmed; da na kasuwanci da masana’antu, Adeniyi Adebayo, da ministar jin kai, Sadiya Farouq, za su bayyana a gaban Kwamitin a ranar Alhamis domin su yi bayani kan zarge-zargen da suke tattare da rabon kudaden.