Kungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NAWOJ) a Jihar Kebbi, ta zabi sabbin shugabannin zartarwa da za su jagoranci gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa a jihar.
Mambobi bakwai da aka zaba su ne Hasana Abubakar-Koko, ta gidan talabijin ta Nijeriya (NTA) a matsayin shugaba, yayin da Sabatu Andrew-Machika daga gidan rediyon Jihar Kebbi, ta zama mataimakiyar shugabar kungiyar.
- Majalisar Dattawa Ta Yi Barazanar Kama Gwamnan Bankin Nijeriya, Emefiele
- Ko Da Gaske Ne Kasar Sin Barazana Ce?
Sauran sun hada da Blessing Michael ta gidan talabijin na jihar a matsayin Sakatariya, Sharifiya Abubakar daga ma’aikatar watsa labaru da al’adu ta jihar a matsayin mataimakiyar Sakatariya, Maimuna Usman daga gidan rediyon Jihar Kebbi a matsayin Sakatariyar Kudi, Maryam Abdullahi-Zuru daga ma’aikatar watsa labaru da al’adu a matsayin ma’ajin kungiyar da kuma Maryam Magana daga gidan rediyon Jihar Kebbi a matsayin mai bin diddigi da binciken kudade.
Alhaji Muhammad Tukur, mataimakin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), shiyyar A, ya ja kunnuwan shugabannin kan jaddada gaskiya da adalci yayin gudanar mulki.
A jawabin karbar sabuwar shugabar kungiyar, Hasana Abubakar-Koko, ta mika godiyarta ga mambobin kungiyar bisa zabinsu, tare da yin alkawarin tabbatar da amincewar da aka yi musu.
“Nasarar da na samu a yau, ta kowane dan kungiya ne, zan tabbatar da na yi aiki da kowa da kowa ba tare da nuna banbanci ko bangaranci na addini da kabilanci ba.
“Na yi alkawarin gudanar da gwamnati ta gaskiya, musamman idan ana maganar yanke shawara, za ta kasance ta bai daya kuma ta gamayya,” in ji ta.
Ta yi alkawarin gudanar da manufar bude kofa, tana mai cewa nata za ta yi kokarin daukar kowane mamba a cikin duk ayyukan da kungiyar za ta gudanar.
Haka kuma za yaba tare da godewa NAWOJ, NUJ da kwamitin tantancewa bisa namijin kokarin da suka yi wajen ganin an gudanar da zaben cikin sauki da kwanciyar hankali.