Ana zargin ‘yan bindiga sun sace wasu matafiya da ba a san adadinsu ba a cikin wata motor haya kirar bas mai dauke da matafiya 18.
An ruwaito cewa, an sace su ne a kan hanyar Ochadamu daura da hanyar Anyigba-Itobe da ke a karamar hukumar Ofu da ke Jihar Kogi.
- Za A Gudanar Da Taron Tunawa Da Jiang Zemin A Ranar Talata Mai Zuwa
- Majalisar Dattawa Ta Yi Barazanar Kama Gwamnan Bankin Nijeriya, Emefiele
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tabbatar ko bas din na dauke da adadin yawan fasinjojin da ya kamata ta dauka ba.
Wani ganau ya ce, lamarin ya auku da karfe misalin 4 na ranar Litinin da ta wuce a kan babbar hanyar, inda ya kara da cewa, bas din ta ta so ne daga gabashin kasar nan zuwa Abuja.
Rahotanni daga yankin sun ce, ‘yan bindigar masu yawa, sun dakatar da bas din ce, inda suka kwashe matafiyan suka shiga daji da su.
Wasu kauyawan da ke a yankin sun ce, ayyukan ‘yan bindigar ya ragu a yankin Ochadamu, amma daga baya ayyukan na suka kara zafafa bayan a rushe wajen da soji ke duba ababen hawa da ke bin hanyar.
An ruwaito cewa, jami’an tsaro da na ‘yan sintiri a yankin na kan kokarinsu wajen kubutar da matafiyan tun bayan aukuwar lamarin.
Kwamdan sojin sama, Jerry Omodara ya ce, mai bai wa gwaman jihar shawara a fannin tsaro, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce, gwamnatin jihar na kokarin ganin an kubutar da matafiyan.
Babu wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yansanda jihar, SP William Aya, ya fitar a kan lamarin.