Tsohon Sanatan da ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya bayyana wa jama’a ya sunayen gwamnonin da ke handame kudaden kananan hukumomi kasar nan.
Buhari dai a ranar Alhamis, ya ce wasu gwamnonin jihohi da jami’an kananan hukumomi su na karkatar da kudaden da suka sace a gudanar da ayyukan raya kananan hukumomi kai tsaye.
- Kasar Sin Na fatan Amurka Za Ta Aiwatar Da Matsayar Da Shugabannin Kasashen Biyu Suka Cimma
- Yanzu-Yanzu: Gobara Ta Tashi A Dakin Kwanan Dalibai A Jami’ar Dan Fodiyo Da Ke Sakkwato
Sani, ya wallafa haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a cewa akwai bukatar shugaba Buhari ya samu kwarin guiwar fitowa ya bayyana sunayen gwamnonin da ke sanya kudaden kananan hukumominsu a aljihunsu.
“Ya kamata shugaban kasa ya kasance mai kwarin guiwa ya fito kawai ya ambaci sunayen gwamnonin da suka makale kason kanananan hukumomi.”
Ko da yake har zuwa yanzu dai gwamonin Nijeriya su 36 sun yi gum da bakinsu kan wannan batu kuma ba su bayyana wa jama’a matsayarsu a kai ba.
A lokacin da aka tuntubi Muhammad Bello, babban sakataren watsa labarai na shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya kuma gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce har yanzu ba su samu wani bayani a hukumance kan wannan batu ba.