Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa a kan Ayyuka na Musamman, Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, ya yi kira ga ‘yan Nigeria da su yi shi rin fuskantar wahalar rayuwa a 2023.
Sanatan, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan zaman kwamitinsa da ministan ma’aikatan jin kai da walwalar al’umma a kan zargin cushe-cushe na Naira biliyan 206 a kasafin kudin ma’aikatan na 2023.
- Wasu Halayen Da Maza Ke Nuna Wa Uwargida In Sun Shirya Kara Aure
- Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Tsige Shugaban NIRSAL, Aliyu Abdulhameed Kan Zargin Almundahanar Kudade
Dan majalisar, ya ce cire tallafin man fetur a shekara mai zuwa zai haifar da tsadar abinci, hauhauwar farashin kayayyakin masarufi tare da tashin farashin man fetur.
Da yake bayani a kan badakala da cushe-cushe da ake zargin an yi a kasafin kudin shekarar 2023, dan majalisar, ya ce kuskure aka samu ba wata badakala ko cushe-cushe bane kamar yadda wasu ke tunani.
Ya kara da cewa saboda haka ne majalisar ta fara binciken kan lamarin.
Ita dai ministar kasafin kudi, Hajiya Zainab Shamsuna ba ta halarci zaman kwamitin ba.