Wasu cikkn jiga-jigai cikin tsohuwar jam’iyyar CPC na fatan jam’iyyar APC ta mika sunan Ministan Shari’a, Abubakar Malami a matsayin wanda zai yi wa dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu mataimaki a zabe mai zuwa na 2023.
Hakan na zuwa yayin da wa’adin da Hukumar Zabe ta kasa INEC ta gindaya na debar wa jam’iyyu domin mika sunayen ’yan takarar Mataimakin Shugaban Kasa, inda jam’iyyun ke ci gaba da fadi-tashi domin ganin cewa ba su yi zaben tumun dare ba.
Hukumar INEC dai ta ce duk jam’iyyar da ba ta mika sunan abokin takararsu zuwa ranar 17 ga watan Yuni, to za a hana ta shiga Babban Zabe mai zuwa.
Rahotanni na cewa jam’iyyar APC da PDP sun takaice zabin abokan takararsu zuwa wasu manyan ‘yan siyasa a wasu sassan kasar nan.
Ana harsashen Jam’iyyar APC zata fito da dan takararta daga yankin Arewa maso gabashin kasarnan, ita kuwa takwararta ta PDP an hasashen nata mataimakin zai fito daga yankin kudu maso kuduncin Nijeriya.
Ko mai dai ya ake ciki lokaci ne kadai zai alkalancin shiyyoyin da mataimakan za su fito.