Tsohon dan majalisar tarayya kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, kamar dan jariri ne idan aka kwatanta nauyin shi da Atiku Abubakar na PDP.
Melaye ya bayyana haka ne a cikin shirin gidan Talabijin na Channels, ashirin nazarin Siyasa.
Ya ce, “A gare mu ‘yan jam’iyyar PDP, mun shawarci Atiku da ya hada jawabinsa na Iashe Zabe, domin shi ne zai zama shugaban tarayyar Nijeriya.
“Bola Tinubu da rashin tsarinsa ba zai yi daidai ba ta kowace irin hanya in aka kwatanta shi da Atiku. Bola Tinubu dan jariri ne kawai idan aka kwatanta shi da Atiku Abubakar a kowane fanni: a fagen siyasa, tunani, zamantakewa, lafiyar jiki, kai har da addini.
“Bola Tinubu da Atiku Abubakar a fagen shaharar siyasa ba su da alaka da juna.Ta yaya Tinubu zai fi Atiku girma? Dangane da gogewar siyasa, ba za ka iya sanya Tinubu da Atiku a shafi guda ba.
“Atiku Abubakar, Tsohon mataimakin shugaban kasar nan ne, don haka yana da gogewar siyasa fiye da Bola Tinubu.”
Melaye ya ci gaba da cewa Atiku ne kawai wanda ya cancanta da ya fi kowa fahimtar matsalolin da Nijeriya ke fuskanta.