Wasu masu Garkuwa da mutane da suka fada cikin komar ‘yansanda a jihar Neja, sun sheda cewa, an tura su ne domin su sace sanata Mohammed Sani Musa, dan jam’iyyar (APC).
An kama su ne a garin Minna a gidan Sanatan wanda a yanzu yake wakiltar mazabarsa ta Neja ta gabas a majalisar Dattawa.
Kakakin rundunar ‘yansanda na jihar DSP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar a jihar a ranar litinin.
Abiodun ya kuma shedawa manema labarai a jihar cewa, ba a san abinda ya sa suka kitsa sace sanatan ba, amma rundunar na ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin, inda ya ce, wadanda ake zargin sun kuma shedawa rundunar cewa, wani mai suna Sherif, wanda a yanzu rundunar ke nema ruwa a jallo ne ya sanar dasu cewa sanatan zai shiga Neja domin halartar taron nadi tare da kuma baiwa sarkin Kagara sandar mulki.
Kakakin ya ci gaba da cewa, runudanar ta kuma kara samun wasu bayanai dangane da binciken da ta gudanar, inda daya daga cikin wadanda aka kama ya ce, Sherif ne ya yi musu jagora zuwa gidan gidan sanatan, inda wadanda ake Zargin suka yi hasashen cewa, sanatan na gidansa bayan ya halarci taron nadin a garin Kagara.