Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana cewar, dama da ikon zabar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC na hannun dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ba Gwamnonin jam’iyyar ba.
Hope, ya bayyana haka ne ga ‘yan jarida a fadar shugaban kasa da ke Abuja jimkadan bayan da suka kammala ganawa da shugaba Muhammadu Buhari kan wasikar da ya aike na neman izinin shugaba Buhari da ya halarci jihar Imo domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta samar.
- Zabar Mataimaki: Buhari Ya Gana Da Gwamnonin APC Kan Fitar Da Mataimakin Tinubu
- Zabar Mataimaki: Akwai Alamun PDP Ka Iya Zabar Muo Aroh Matsayin Mataimakin Atiku
Ya ce, akwai bukatar jam’iyyar ta yi zurfin nazari wajen duba hadin kai da adalci ga kowani yanki na kasar nan wajen zabar mataimakin shugaban kasa.
Dangane da kace-nace din da ke ta yi cewa tikitin Musulmi da Musulmi, ya ce, babu wani wuri a kundin tsarin mulkin kasa da aka nuna batun addini wajen waye zai zama Shugaban Kasa ko mataimakin.
Sai dai ya ce, ana duba hanyoyin da za su tabbatar da hadin kai da cigaban kasa ne a kowani lokaci wajen tafiyar da harkokin da suka shafi gwamanti da mulki.
“Damar dauka da zabar mataimakin shugaban kasa na hannun dan takarar da aka zaba ne,” Uzodimma ya fada.